'Yan adawa a majalisar Niger na neman bayani kan kuɗaɗen tsaro

Majalisar ta goyi bayan shirin gwamnati na yaki da almundahana Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Majalisar dokokin Nijar ta bude zamanta na bana

A jamhuriyar Nijar, majalisar dokokin kasar ta bude zamanta na bana, har ma 'yan adawa suka nemi gwamnati ta bayyana yadda ta kashe kuɗaɗen tsaron ƙasar.

'Yan adawar sun nuna damuwa game da kisan da ake zargin 'yan tada-kayar-baya na yi wa sojojin kasar, don haka suka ce sai gwamnati ta yi bayani a kan yadda ta sarrafa kudin da majalisar ta ware don harkokin tsaro.

Jagoran adawa a majalisar, Honourable Soumanou Sanda na jam'iyyar Model Lumana ya ce suna buƙatar majalisar ta nemi ƙarin bayani daga gwamnatin kan dalilin da ya sa ake ci gaba da kashe sojojin ƙasar, ba kawai ta nuna damuwa abu ya wuce kenan ba.

Ya ce abin takaici ne yadda har yanzu jamhuriyar Nijar ke ci gaba da binne sojojinta sakamakon kisan da 'yan tada-ƙayar-baya ke yi musu.

Shugaban majalisa dokokin kasar Usaini Tinni ne ya bude zaman majalisar da zai dauki tsawon wata uku ana gudanarwa don tattauna ƙudurorin dokoki da gwamnati ta gabatar.

Malam Usaini Tinni ya nuna goyon bayan shirin gwamnati na yaki da almundahana.

Bayan yin na'am da dokokin, ana sa ran 'yan majalisar za su rika gayyatar wasu jami'an gwamnati lokaci zuwa lokaci don bayar da bahasi kan yadda suke gudanar da wasu ayyuka.

Za kuma a rika shirya wa 'yan majalisar tarukan bita, domin ilmantar da su don sanin makamar aiki.

Labarai masu alaka