Harin iska mai guba ya jikkata fararen hula a Iraqi

Iraqi Mosul Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'an Amurka da Iraqi na zargin kungiyar IS da amfani a makamai masu guba

Fararen hula 12 ne suka samu raunuka a kasar Iraqi, a wani harin da aka bayyana cewa na sinadarin iskar gas mai guba ce a kan birnin Mosul.

An harba wasu rokoki ne a birnin wanda har yanzu mayakan IS ke iko da bangaren yammacinsa, ko da yake, ya zuwa yanzu ba a ce ga wanda ya kai harin iskar gas mai warin gasken ba.

Rundunar sojin Iraqi ta ce ta yi amanna mayakan IS na sarrafawa tare da ajiye iskar gas ta Chlorine.

Cikin fararen hular da suka jikkata har da wani yaro mai shekara 11 da ya samu mummunar kuna, da kuma wani jariri dan wata daya da haihuwa.

Kwamitin kasa da kasa na kungiyar Red Cross ya yi Allah wadai da amfani da makaman masu guba.

Image caption Fararen hula 12 suka jikkata a harin makamai masu guba a Mosul

Daraktan kungiyar ta Red Cross a yankin gabas ta tsakiya Robert Mardini, ya ce ana yi wa mutanen da suka jikkata magani a asibiti.

Ya ce Marasa lafiyar na cikin matsanancin hali, amma ana ba su kulawar da ta kamata.

Mr Mardini ya kuma ce amfani da makamai masu guba, haramtaccen abu ne a dokokin kasashen duniya.

An dai dade ana zargin kuniyar ta IS da sarrafawa tare da amfani da makamai masu guba a yankunan da take rike da su na Iraqi da makwabciyarta Syria.

Labarai masu alaka