Tanzaniya ta ɗaure 'Shaiɗan' a gidan yari

Elephant Poacher Hakkin mallakar hoto TERRA MATER FACTUAL STUDIOS
Image caption Mafaraucin giwar wanda aka fi sani da Shaiɗan ya daɗe yana kauce wa kamu

Hukumomi a Tanzaniya sun ɗaure wani mafaraucin giwa mai laƙabin "Shaiɗan" bayan ya yi ƙaurin suna, tsawon shekara 12 a gidan yari.

Wata hukumar kare namun daji, ta ce Boniface Matthew Maliango shi ne da alhakin kashe dubban giwaye.

An kama shaiɗan ne cikin watan Satumban 2015 a birnin Dar es Salaam bayan an shafe tsawon lokaci ana farautarsa.

Laifukansa su ne alkiblar da aka shirya wani fim mai suna, The Ivory Game wanda fitaccen jarumin fina-finan Hollywood Leonardo DiCaprio ya shirya.

Hakkin mallakar hoto ART WOLFE
Image caption Ƙasashe da dama a Gabashin Afirka na da albarkar giwaye

A harshen Swahili ana yi wa Maliango laƙabi da sunan Shetani, wato Shaiɗan.

Wata ƙungiya mai fafutukar kare namun daji ta Elephant Action League ta ce Maliango na jagorantar wani gungun masu safarar hauren giwa a faɗin ƙasa biyar da suka hadar da Tanzania da Burundi da Zambia da Mozambique da kuma kudancin Kenya.

An ɗaure Shaiɗan tare da 'yan'uwansa, Lucas Mathayo Maliango da Abdallah Ally Chaoga.

An kama su ne a lokacin da suke yunƙurin fasa-ƙwaurin haurukan giwa na kuɗi sama da dala dubu 850.

An zargi Maliango da safarar hauren giwa ga wata 'yar ƙasar China Yang Fenglan, wadda aka fi sani da suna "Sarauniyar Hauren giwa", da ke fuskantar shari'a a ƙasar Tanzania kan safarar hauren giwa sama da 700 da kuɗinsu ya kai dala miliyan 2.5.

Masu kare namun daji sun ce buƙatar da ake yi wa hauren giwa a China ta janyo ƙaruwar haramtacciyar farautar giwa.

Ko da yake, an haramta saye ko sayar da hauren giwa a tsakanin kan iyakokin ƙasashen duniya, amma ana bari a cikin wasu ƙasashe.

Labarai masu alaka