Osinbajo ya rantsar da Onnoghen babban alkalin Nigeria

Onnoghen Hakkin mallakar hoto Channels
Image caption Onnoghen ya ce ba lallai bane kowane dan Najeriya ya ga alkali ba kafin gaskiya ta yi halinta

Mukaddashin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya rantsar da Walter Onnoghen a matsayin babban alkalin kasar, bayan da majalisar dattawa ta amince da nadinsa.

Da safiyar ranar Talata ne aka rantsar da Mista Onnoghen a dakin taro na fadar shugaban kasa.

A watan Nuwamba ne Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Mista Onnoghen, wanda dan jihar Cross Rivers ne, a matsayin alkalin alkalai na riko bayan da Mahmoud Mohammed ya yi ritaya.

Mista Osinbajo ya ce Shugaba Buhari ya umarce shi ya shaida wa sabon mai shari'ar cewa ya samu aikin ne a lokacin da "jama'a ke kara nuna rashin amincewa da bangarorin gwamnati da dama".

Ya kuma nuna kwarin gwiwa cewa Mista Onnoghen zai taimaka wurin farfado da yardar da jama'a ke da ita kan gwamnati.

Nadin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da bangaren shari'ar ke fama da manyan matsaloli.

Manyan alkalai da ma'aikatan kotu da dama na fuskantar shari'a kan zargin cin hanci da rashawa.

Da yake magana a wurin rantsar da shi, mai shari'a Onnoghen ya ce zai yi aiki domin kare tsarin mulkin kasar.

Sannan ya kara da cewa zai nemi tallafin dukkan 'yan kasar domin cimma burinsa na kawo sauyi a fagen shari'ar kasar.

'Za mu karfafa 'yancin da muke da shi'

Hakkin mallakar hoto Nigerian Government
Image caption Shugaba Buhari ya nada Mista Onnoghen a matsayin alkalin alkalai na riko bayan da Mahmoud Mohammed ya yi ritaya

A jawabin da ya yi a gaban majalisar dattawa lokacin tantance shi, Onnoghen ya ce zai yi kokari domin ganin ya kara karfafa sashen shari'a a matsayin wani bangare mai cin gashin kansa.

Sanatoci sun tambaye shi yadda zai tabbatar da adalci ga talakawan Najeriya da kuma yadda zai tabbatar da yin shari'ar wadanda aka kama da laifin cin hanci ba tare da an bata lokaci ba.

Onnoghen ya yarda da batun da 'yan majalisar dattawa suka yi na cewa akwai cin hanci a bangaren shari'ar, amma ya kara da cewa zai kasance daya daga cikin matsalolin da zai magance.

"Za mu yi aiki domin tabbatar da haka kuma za mu kara karfin gwiwa wajen tabbatar da gaskiya a ayyukanmu," a cewar Onnoghen.

Sabon Babban jojin kasar, ya kuma yi magana a kan yadda zai karfafa bangaren shari'ar kasar a matsayin wani bangare na gwamnati mai zaman kansa wanda zai kasance wuri na karshe da 'yan Najeriya baki daya za su yi fatan samun adalci.

Kamar yadda ya furta, ba lallai bane sai ko wane dan Najeriya ya ga alkali ba kafin gaskiya ta yi halinta ba.

Onnoghen ya shaida wa sanatocin cewar: "Za mu karfafa 'yancin da muke da shi. Ba zan yi sake da wannan ba."

Labarai masu alaka