Sa'o'i kaɗan suka rage a rufe filin jirgin saman Abuja

An soki matakin rufe filin jirgin Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kamfanonin jiragen sama da 'yan kasuwa sun soki matakin rufe filin jirgin

Zuwa karshen ranar Laraba, Abuja, babban birnin Najeriya, zai kasance ba shi da filin jirgin sama da jirage za su rika tashi tare da sauka a ciki.

Gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin a rufe filin jirgin saman domin a gyara titunan shi wanda ya kamata a ce an yi musu gyara tun shekara 15 da suka gabata.

A bara ne dai wani jirigin saman Afirka ta kudu ya lalace a lokacin da ya sauka sakamakon ramukan da ke kana titunan.

A cikin sao'i kadan masu zuwa, jirgi na karshe zai sauka a babban birnin Najeriyar har sai bayan akalla mako shida.

Daga ranar Laraba ne fasinjoji za su rika tashi daga filin jirgin sama da ke jihar Kaduna.

Sai dai za su rika bin hanyar da ke tattare da hadarin sace mutane.

Za a rufe filin jirgin saman Abuja

Duk da cewa gwamnati ta karfafa matakan tsaro, matafiya 'yan Najeriya da dama sun damu kwarai.

Mafi yawancin kamfanonin jiragen sama wadanda suka hada da kamfanin jirgin saman Burtaniya, British Airways ba za su rika zuwa Kaduna ba saboda yanayin tsaro.

Dangane da yadda matafiya suka ji da wannan sauyin, Naziru Mika'ilu ya tambayi Alhaji Abubakar Mohammad Kangiwa yadda wannan sauyin zai shafi harkokinsa, a inda ya ce zai fuskanci asara.

Ya kuma ce zai daina amfani da jirgi har sai an kammala gyaran filin jirgin na Abuja.

Ku saurare shi domin jin dalilinsa na daina amfani da jirgin.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Alhaji Abubakar Mohammad Kangiwa

Labarai masu alaka