Nigeria: Kotu yanke wa 'yan sanda hukuncin kisa

Yan sandan Nigeria Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An sha zargin 'yan sandan Najeriya da take hakkin bil'adama amma suna musantawa

Wata kotun tarayya a Najeriya ta yanke wa wasu 'yan sanda biyu hukuncin kisa bayan da ta same su da laifi a kisan wasu 'yan kasuwa shida a Abuja, babban birnin kasar.

Alkalin kotun Ishaq Bello ya ce Ezekiel Acheneje da Baba Emmanuel sun taka rawa wurin kisan matasan 'yan kabilar Igbo, wadanda ke hanyar su ta komawa daga wurin wata liyafa a shekarar 2005.

Kotun ta kuma wanke Danjuma Ibrahim da Nicholas Zakariah da kuma Sadiq Salami daga hannu a cikin lamarin wanda ya faru a unguwar Apo.

Wadanda aka kashe din dai wasu 'yan kasuwa ne da suka hada da mace - shekarunsu sun kama daga 21 zuwa 25.

'Yan kasuwar da aka kashe su ne: Ifeanyi Ozor, Chinedu Meniru, Isaac Ekene, Paulinus Ogbonna, Anthony Nwodike da kuma Augustina Arebun.

Mutanen da aka yanke wa hukuncin na cikin mutum shida da aka samu da kisan 'yan kasuwar saboda zarginsu da kasancewa 'yan fashi.

Har yanzu ana neman mutum na shida, Othman Abdulsalam, wanda shi ne shugaban ofishin 'yan sanda na Apo a lokacin, bayan ya tsere.

Kawo yanzu babu wani martani daga mutanen biyu ko kuma rundunar 'yan sandan Najeriya.

Yadda lamarin ya faru

Lamarin ya faru ne a daren ranar bakwai ga watan Yunin shekarar 2005 lokacin da 'yan kasuwar da ke sayar da kwance kayan ababen hawa ke kan hanyarsu komawa gida daga wurin wani biki Apo, amma 'yan sanda suka tare su a wani wurin binciken abubuwan hawa.

'Yan sanda sun yi zargin cewa 'yan kasuwar 'yan fashi ne kuma sun harbe su ne bayan da suka yi yunkurin tserewa.

Sai dai wani kwamitin bincike da shugaban kasar na wancan lokacin Cif Olusegun Obasanjo ya kafa -- bayan an yi ta ce-ce-ku-ce kan batun -- ya gano cewa 'yan sandan karya suke yi, kana ya bayar da shawarar a tuhume su da laifin kisan kai.

An kashe shekara 12 ana wannan shari'a, inda daga kashe aka yanke hukuncin kisa kan 'yan sandan biyu, yayin da aka wanke uku, amma daya daga cikin su ya tsere kuma ana ci gaba da nemansa.

Labarai masu alaka