Wata mai ciwon ajali tana nema wa mijinta matar aure

Amy Rosenthal
Image caption Marubuciyar ta zauna da mijinta tsawon shekara talatin kuma tana ganin ya cancanci samun wata matar bayan mutuwarta

Wata marubuciya da ta gamu da sankarar mahaifa kuma likitoci suka ce ta ajali ce, ta rubuta taƙaitaccen kundin halayen mijinta ta yadda zai samu "wata mai ƙaunarsa".

Amy Krouse Rosenthal ta zayyana nagartattun halayen mai gidanta Jason kuma ta ce tana fatan "wadda ta dace za ta karanta kuma ta samu...".

Ta rubuta a jaridar New York Times cewa "Ni ban taɓa shiga shafukan sada zumunta na neman abokin zama ba, amma dai zan wallafa bayanin halayen Jason, bisa la'akari da zamana da shi kamar tsawon kwana 9,490."

Amy fitacciya ce wajen rubuta litattafan koyon rubutu na yara, da kuma kissoshin dangi da rayuwarta.

Kimanin shekara talatin kenan suna tare da mai ɗakinta har ma suna da 'ya'yan da sun manyanta.

A ƙarshen rubutun nata mai taken 'Ko kina son aurar mijina' Amy ta ce: "Ina dunƙule wannan gangariyar kyauta a ranar tunawa da masoya ta Valentine, wadda nake fatan cewa wata da ta dace za ta karanta, kuma ta samu Jason, da nufin fara wani sabon zaman soyayya."

"Zan bar muku wannan sarari da gangan a nan ƙasa don ba ku, ku biyun sabon mafarin da kuka cancanci samu."

Daga nan sai wani farin fili ya biyo a ƙasan rubutu.

Ta kammala da: "Ga duk soyayyata nan, Amy."

Labarai masu alaka