'Bai kamata barazana ta hana Buhari ziyara ba'

Nigeria Vice President Osinbajo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Osinbajo yana aiki tuƙuru da kuma ɓullo da wasu matakan da wasu ke cewa sun janyo kyautatuwar al'amura a baya-bayan nan.

Ana samun ce-ce-ku-ce a baya-bayan nan tsakanin 'yan Nijeriya kan ziyarce-ziyarcen da muƙaddashin shugaban ƙasar, Farfesa Osinbajo ke kai wa wasu sassa.

Masu sharhi na ganin ziyarar da ƙarin wasu matakai sun taimaka gaya wajen samun kyautatuwar harkokin tattalin arziƙi da zamantakewar al'umma, baya ga inganta alaƙa tsakanin gwamnati da jama'ar da ake mulka.

Wani mai sharhi kan harkoki a Nijeriya, Ja'afar Ja'afar na ganin, ziyarar ta taimaka wajen bunƙasa yawan man fetur ɗin da Nijeriya ke haƙowa a yankin Naija Delta, wanda a baya ya yi fama da ayyukan matasa tsageru masu fasa bututan mai da iskar gas.

A ƙarshen watan Fabrairu ma, Osinbajo ya kai ziyarar ba-zata ɗaya daga cikin filayen jiragen saman ƙasar da ke Lagos, har ya kewaya wasu sassa don ganin halin da suke ciki.

Ya kuma kai irin wannan ziyara zuwa kudancin jihar Kaduna mai fama da hare-haren da ake alaƙanta su da ƙabilanci, har ma ya bai wa mutanen da abin ya ritsa da su tabbacin ɗaukar matakai don kawo ƙarshen rikicin.

A baya, wasu masu sharihi sun sha sukar shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari a kan rashin ziyartar sassan ƙasar don ganin halin da al'umma ke ciki.

Image caption An yi wa shugaba Muhammadu Buhari addu'o'in samun lafiya a coci-coci da masallatai da ke fadin kasar.

Ja'afar Ja'afar ya ce "karo biyu shugaba Muhammadu Buhari yana shirya kai ziyara zuwa yankin Naija Delta, amma sai ya fasa sakamakon barazana daga tsagerun matasan yankin".

A cewarsa kamata ya yi shugaban ya yi amfani da dabarun mulki wajen shawo kan tsagerun ta yadda za su riƙa yi masa maraba maimakon kashedin kada ya kai ziyara.

Masharhancin ya ce wasu makusantan shugaba Buhari ba za su ji daɗin irin wannan ziyara da muƙaddashin shugaban yake kai wa ba, don kuwa a cewarsa ziyarar na fito da gazawar Buhari ne ƙarara.

Ya ce magoya bayan Muhammadu Buhari za su so a ce shugaban ne yake kai wannan ziyara da kansa, maimakon muƙaddashinsa abin da a siyasance ke ƙara fito da ƙimar Osinbajo.

Fadar shugaban Nijeriya dai ta yi watsi da irin waɗannan raɗe-raɗi da ake yaɗawa inda ta ce muƙaddashin shugaban ƙasar ba ya yin wani abu sai ya tuntuɓi shugaba Muhammadu Buhari.

Labarai masu alaka