Mutum miliyan biyar na bukatar agajin abinci a Somalia

Somalia Garowe Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu sabbin kaburbura a wajen wani sansanin 'yan gudun hijira da ke birnin Garowe na kasar Somalia

Mutum 110 ne yunwa ta hallaka cikin kwana biyu a yanki daya kacal na Somalia, sakamakon wani matsanancin fari da ke barazana ga rayuwar miliyoyin mutane a fadin kasar.

Mutanen sun mutu ne a kudu maso yammacin yankin Bay na Somalia.

A ranar Talata, shugaban kasar Somalia Mohamed Abdullahi Farmajo, ya ayyana farin a matsayin wani babban bala'in da ya shafi kasa.

Majalisar Dinkin Duniya ta kididdige cewa 'yan Somalia miliyan biyar ne ke bukatar agajin abinci.

Ta kuma sanya Somalia a matsayin daya daga cikin kasa hudu da ke fuskantar barazanar karancin abinci da ja'ibar yunwa.

Sauran kasashen su ne Najeriya, da Sudan ta Kudu da kuma Yemen.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Karancin ruwan sha da na abinci ya sanya ganin mushen dabbobi kamar wannan saniyar warwatse a ko ina

Wannan adadin daga kudancin yankin Bay shi ne kiyasi na farko da hukumomi suka sanar.

Matsalar karancin abinci a Somalia akasari ta faru ne saboida rashin saukar ruwan sama sakamakon sauyin yanayin nan na El Nino, da ya shafi gabashi da kudancin Afirka.

Dabbobi ma na ta mutuwa saboda wannan bala'i, inda ake ganin gawawwakinsu yashe a hanyoyi.

Mutane kusan dubu 260 ne suka mutu a lokacin da kasar Somalia ta fada cikin matsalar karancin abinci daga shekarar 2010 zuwa 2012.

Karin wasu dubu 220 sun mutu a lokacin wani karancin abinci da kasar ta fada a 1992.

Labarai masu alaka