'Dubban jama'ar Diffa a Nijar na bukatar dauki'

Jihar Diffa na bukatar agajin gaggawa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jama'ar jihar Diffa a jamhuriyar Nijar sun fada cikin talauci saboda matsalar tsaro

Wasu yan majalisar dokokin jamhuriyar Nijar na ci gaba da yin kira ga hukumomi da kungiyoyin agaji na ciki da wajen kasar su kai wa jihar Diffa dauki.

Sannu a hankali dai kwanciyar hankali ya fara tabbata a yankin, ko da yake, har yanzu tattalin arzikin jihar da rayuwar al'umma na cikin wani hali.

Dan majalisar dokokin Nijar daga jihar Diffa Bulu Mamadu, ya ce har yanzu mutane a jihar Diffa na cikin fargaba.

Ya ce akwai bukatar a kula da al'ummomnn da ke wannan yanki, musamman 'yan gudun hijarar da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu.

Dan majalisar ya ce dubban jama'ar da suka saba noma ne suka shiga mawuyacin hali a yankin saboda tashin hankali ya hana su gudanar da sana'arsu.

Hakan ya haifar da matsalolin karancin abinci da kuma Yunwa a tsakanin al'umma.

Labarai masu alaka