Ba mu yarda Obama ya yi wa Trump kutse ba — FBI

Shugaban Amurka, Donald Trump Hakkin mallakar hoto Huw Evans picture agency
Image caption Trump ya ce Obama ya bayar da umarni a yi wa wayarsa kutse

Shugaban Hukumar Binciken Laifukan cikin gidan Amurka, FBI, James Comey ya yi watsi da batun Donald Trump cewa Obama ya yi wa wayarsa kutse.

A ranar Asabar ne dai shugaba Trump ya yi zargin cewa magabacinsa, Barack Obama, ya yi masa a wayarsa.

Rahotanni sun ce Mista Comey ya nemi bangaren shari'ar kasar da ya yi watsi da batun da Donald Trump yake yi cewa mista Obama ya yi masa kutse a lokacin kamfe na zaben kasar na 2016.

Jaridar New York Times ce dai ta rawaito wannan labari, a inda kamfanin NBC ya tabbatar da shi.

Har kawo yanzu dai bangaren shari'ar bai fitar da wata sanarwa ba kan batun.

Mista Trump dai ya yi zargin ne ta hanyar wallafawa a shafinsa na twitter.

Wani mai magana da yawun mista Obama ya ce zargin 'shaci fadi ne kawai'.

Karin bayani