'Birtaniya ta yi min ƙaryar ƙin ceto 'yan matan Chibok'

Boko Haram
Image caption Har yanzu mafi yawan 'yan matan Chibok na hannun kungiyar Boko Haram

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi watsi da wani rahoto da wata jaridar Birtaniya ta wallafa da ke cewa ya ƙi amincewa da tayin da rundunar sojin sama ta Birtaniyan ta yi masa, na ceto 'yan matan makarantar Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace.

Wata majiya da ke da hannu cikin neman 'yan matan ta shaida wa jaridar Observer cewa, "A makonnin farko da aka sace 'yan matan mun gano inda suke. Mun yi wa gwamnatin Najeriya tayin ceto su, amma sai ta ki bayar da hadin kai."

Amma mai magana da yawun Mista Jonathan din Ikechukwu Eze, ya yi watsi da zargin, yana mai cewa ƙarya ne.

A wata sanarwa da ya fitar Mista Eze ya ce, "Gaba-gadi za mu iya cewa wannan rahoto ƙarara ƙarya ce."

Ya ce hadin gwiwar da aka yi tsakanin wasu ƙasashen duniya domin ceto 'yan matan ya hada da maƙwabtan Najeriya ne kawai, kuma shugaba Jonathan a lokacin ya yi ta goyon bayan tallafinsu, ya kuma ƙyale sojojin ƙasashen yamma sun yi zagaye da jiragen sama a sararin samaniyar ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta ambato Mista Eze yana cewa, "Amma ba mu yi mamakin jin wannan shaci-fadin ba a daidai wannan lokacin, saboda yadda wasu mutane ke saka siyasa a lamarin ceto 'yan matan Chibok domin wani buri nasu na daban."

Goodluck Jonathan ya musanta karbar cin hanci

Wani mai magana da yawun gwamnatin Najeriya mai ci kuwa, ya shaida wa BBC cewa, rahoton jaridar Observer ya tabbatar da zargin da dama can suke yi wa Mista Jonathan, cewa yana saka siyasa a lamarin ƙungiyar Boko Haram.

'Jonathan ya sayo jabun makamai'

A watan Afrilun 2014 ne mayakan kungiyar Boko Haram suka sace 'yan matan makarantar sakandiren Chibok da ke jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya, sama da 200, daga cikin makarantarsu.

A wancan lokaci dai jim kadan bayan sace 'yan matan, gwamnatin Najeriya ƙarƙashin shugaba Goodluck Jonathan ta musanta lamarin, amma daga bisani ta yarda, al'amarin da ya jawowa gwamnatin suka sosai daga cikin ƙasar da ma wasu manyan ƙasashen duniya.