An daure tsohon gwamnan Adamawa shekara biyar a kurkuku

James Ingilari Hakkin mallakar hoto Premium Times
Image caption An gurfanar da James Ingilari gaban kotun ne ranar 21 da watan Satumban 2016

Wata babbar kotu a jihar Adamawa da ke Najeriya ta yanke wa tsohon gwamnan jihar James Bala Ingilari, daurin shekara biyar a gidan kaso saboda sabawa ka'idojin bayar da gwangila.

Alkalin kotun Nathan Musa ya samu tsohon gwamnan da aikata laifuka hudu daga cikin biyar din da aka tuhu me shi.

Kotun ta kuma yi watsi da tuhumar da aka yi wa tsohon sakataren gwamnatin jihar da kuma kwamishinan kudi dangane da tuhumce-tuhumcen da aka musu.

Shi ne gwamna na biyu da aka taba daurewa bisa zargin cin hanci da rashawa tun bayan da kasar ta koma tafarkin demokuradiyya a 1999.

Mista Ingilari ya shaida wa manema labarai a wajen kotun cewa bai amince da hukuncin ba, kuma zai daukaka kara.

Mai shari'a Musa ya ce doka ta tanadi cewa bai kamata a bai wa mai laifin damar biyan tara ba.

Sannan ya kara da cewa Mista Ingilari na da damar zabar kurkukun da yake so domin yin zaman wakafin nasa.

Muhimmancin hukuncin, Ibrahim Isa, BBC Abuja

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wannan kara dai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ce ta shigar.

Kuma masu sharhi a kan al`amura na ganin cewa wannan hukuncin yana da muhimmanci, saboda a ganinsu, wannan babban misali ne dangane da ikirarin da kowane bangaren gwamnati ke yi a Najeriya na dukufa wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Ba kasafai ake yanke wa manyan jami`an gwamnati hukunci ba, kuma ana zargin hakan na da nasaba da jan shara`a har tsawon wani lokaci inda akan shiriritar da magana.

A yanzu haka ana da shara`ar wasu tsofaffin gwamnoni da ake yi tun farkon komawar Najeriya ga turbar demokuradiyya, amma har yanzu ba a kai ga yanke hukunci ba.

An gurfanar da Mista Ingilari ne a gaban kotun a ranar 21 da watan Satumban 2016.

Labarai masu alaka