'Yan Nigeria su guji zuwa Amurka a yanzu'

Buhari Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Abike Dabiri-Erewa ta ce jinkirin ya zama dole ganin rashin tabbas na manufar shige da ficen sabuwar gwamnatin Amurka

Gwamnatin Najeriya ta shawarci masu niyyar zuwa Amurka a yanzu su dage balaguronsu har sai Amurka ta warware zare-da-abawa kan sabuwar manufar shige-da-ficenta.

A wata sanarwar da Mai taimaka wa shugaban Najeriya ta musamman kan harkokin 'yan kasar da ke kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa ta fitar, ta ce ya zama dole ta yi gargadin domin ganin irin rahotannin da ke zuwa ofishinta.

Misis Erewa ta ce, "A makonnin da suka gabata, ofishin ya samu rahotannin da ke cewar ana hana 'yan Najeriya masu takardun izinin zuwa Amurka shiga kasar, inda aka dinga mayar da su Najeriya."

"A rahotannin da ofishin ya samu, an gaggauta tasa keyar mutanen da lamarin da ya rutsa da su gida, kuma aka soke takardunsu na izinin shiga Amurkar," in ji ta.

Ta kara da cewa, "Babu wata hujjar da aka bayar kan matakin da hukumomim shige-da-ficen Amurka suka dauka."

A karshe tatunasar da 'yan Najeriya da ke zama a kasashen ketare bukatar yin da'a da bin dokokin kasashen da suke zama, su kuma zama jakadun kasarsu na gari a can.

Dama dai tun bayan da shugaba Donald Trump ya hau karagar mulkin Amurka ake ta dari-darin ko umarnin da ya bayar na hana 'yan wasu kasashe bakwai shiga kasar zai shafi 'yan Najeriya.

Sai dai kuma daga baya ofishin jakadancin Amurka a Najeriyar ya fitar da sanarwa cewa al'amarin ba zai shafi Najeriya ba.

Amma dama masu sharhi suna ta kokonta cewa zuwa wani lokaci can gaba, Amurkar na iya hana ko kuma rage kwararar 'yan Najeriya cikin kasar.

Cikin 'yan Afirka da dama da suke ci-rani a Amurka ya duri ruwa, don fargabar ko sabbin dokokin Mista Trump na hana kwararar baki da 'yan ci-rani musamman daga nahiyar da kuma Gabas ta Tsakiya zai shafe su.

Hakan tasa wasu da yawa suka dinga ketarewa zuwa kasar Canada don gudun kada a rabo su da nagiyar Amurkan gaba daya ba tare da sun shirayawa yin hakan ba.

Labarai masu alaka