Gurbatacciyar iska ta fi HIV da Ebola illa ga dan adam

Logan Eddy
Image caption Wani ma'aikacin sa kai, Logan Eddy na kokarin samar da wata hanya da za ta magance ko takaita gurbataccen hayaki

Babbar darakta a hukumar lafiya ta duniya WHO, ta yi gargadin cewa gurbacewar iska na daya daga cikin babbar barazana ga lafiyar al'ummar duniya.

A wata hira da BBC, Margaret Chan, ta ce gurbatacciyar iskar da ake shaka ta fi illa ga lafiyar al'umma a kan cutar Ebola da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV, kuma sannan tafi illa ga matasa.

Dr Chan ta ce kididdigar da aka yi a baya-bayan nan ta nuna cewa yara 600,000 ne 'yan kasa shekara biyar suka mutu a duniya, sakamakon cututtukan da suka shafi numfashi kamar numoniya da asma.

Daga nan ta yi kira ga gwamnatocin kasashe da su dauki matakan gaggawa wajen magance wannan matsala ta gurbacewar iska.

Ya ya za a magance matsalar?

An samu ra'ayoyi mabanbanta kan hanyar da ya kamata a bi don rage dumamar yanayi, ciki akwai masu sauki, da masu tsauri.

Wani ma'aikacin sa kai mai suna Logan Eddy, ya fara nazari don lalubo hanyar da za a magance shakar gurbatacciyar iska.

Ya yi wata doguwar tafiya a hanyoyi daban-daban, da tituna manya da kanana, inda ya gano yadda motoci ke fitar da iska gurbatacciya wadda yawan shakar ta babbar illa ce ga lafiyar bil adam.

Tuni wasu biranen kasashe suka fara daukar matakai na kashin kansu, don rage gurbatacciya iskar.

Cutar mantuwa ta fi kama masu zama daf da titi — Bincike

Misali wata makarantar firamare a birnin Landan ta sanar da cewa watakila ta kafa dokar sanyawa dalibai abin rufe hanci, don kariya daga shakar gurbatacciyar iska.

Hukumomin yankin Cornwall sun ce za su kwashe mutanen da gidajensu ke bakin hanyoyin da ake yawan zirga-zirga.

Yayin da biranen Paris, da Mexico, da Madrid za su dauki matakin haramta amfani da man dizel daga shekarar 2025.

Kididdigar hukumar lafiya ta duniya WHO, ta gano kashi 92 cikin 100 na al'umar duniya na shakar gurbatacciyar iska.

Haka kuma gurbatacciyar iskar da masu karamin karfi ke shaka ta na samuwa ne daga itacen girki.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Birnin Delhi na kasar India shi ya fi kowanne gurbatacciyar iska a duniya

A kasashe masu tasowa, iskar da ababen hawa ke fitarwa da kuma ta masana'antu, su kan hadu sun bayar da gurbatacciyar iska.

A lokacin da Logan ya tsaya a wasu manyan tituna, sai ya gano illar gurbatacciyar iska ta fi wadda hukumar lafiya ta duniya ta bayyana.

Idan mutum na tsaye a bakin titi ko manyan hanyoyi a lokacin da ya ke jiran ketara hanya, iskar da yake shaka kadai a wurin cikin 'yan mintina kalilan ta isa haddasa matsala ga lafiyarsa.

Amma mutane za su iya kaucewa irin wannan matsala, ta hanyar daina tsayawa kusa da tashar mota da wurin da hada-hadar inijinan motoci ke da yawa.

Image caption Matafiya za su iya gano ta inda gurbatacciyar iska ke fitowa

A yankin Leicester na Ingila kuwa an samar da wata na'ura, da za ta nunawa mutane wuraren da hayaki gurbatacce ke fitowa da kuma lokutan da aka fi samu.

Wani farfesa a jami'ar Leicester ya ce gano lokutan da hayakin ya fi yawa, da wuraren da yake fitowa, wanda hakan zai taimaka matuka wajen rage shakar iskar da ke haddasawa dan adam illa ga lafiyarsa.

Farfesa Roland Leigh ya ce daya daga cikin hanyoyi mafi sauki da za a iya magance matsalar ita ce, mutane su inganta harkokin sufuri, saboda idan aka samu cunkuson ababen hawa a kusa da makarantu ko gidan tsofaffi, ba za a samu iskar da za ta yi musu illa ba.

'Gurbatacciyar iska ce babbar barazanar kiwon lafiya'

Bishiyoyi na rage gurbatar yanayi

Wanke injin mota

A kasashen Turai, fiye da shekara 10 kenan aka tilastawa mutane wanke injin mota, haka injinan motocin masana'antu, kuma hakan ya yi tasirin rage gurbataccen hayaki.

Image caption Jami'ar Bath ta yi wani bincike kan illar da gurbatacciyar iskar da motoci ke fitarwa ke haddasawa al'uma

Kwararrun injiniyoyi na jami'ar sun dauki lokaci mai tsawo su na nazari, daga karshe sun amince idan har ana wanke ijinan motoci yadda ya kamata, za a rage yawan gurbatacciyar iska.

Wata karin matsalar da suka gano, ita ce har yanzu tsofaffin motocin da injinansu suka tashi daga aiki su na ci gaba da kaikawo a titunan birane.

Matakin sauya tsoffin motocin abu ne mai matukar wahala, saboda batu ne ake yi na kudi.

'Afirka bata hoɓɓasa raguwar gurɓatacciyar iska'

A yawancin kasashen nahiyar Afirka, babu wata alama da ta nuna ana kokarin samar da wata hanya don gano yawan hayakin da motoci ke fitarwa.

To amma kasar Ghana ta fara wani wani gangami a shafin sada zumunta na Twitter mai tambarin 'soicanbreath' domin fadakar da al'umma kan illar gurbatar mahalli sakamakon hayakin da ake shaka daga murhu.

Gurbatacciyar iska ta lahanta mutane a Kaduna

Wata kungiya mai zaman kanta a kasar mai suna, Global Alliance ta fara kokarin sauya tunanin mutane domin fara amfani da wani sabon tsari da ba shi da hadari ga lafiya.

Za a rage fitar da gurbatacciyar iska

Masana kimiyya dai sun ce dole iskar da ake fitarwa ta ragu sosai, domin a samu daidaito a yanayin muhalli.

Wannan ne makon da aka ware domin fadakarwa a kan illar gurbatacciyar iska ga al'umma.

Labarai masu alaka