Donald Trump ya kafa sabuwar dokar hana shiga Amurka

Shugaban Amurka, Donald Trump Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Sabuwar da Shugaba Donald Trump ya rattaba wa hannu za ta fara aiki ne a 16 ga Maris

Shugaban Amurka, Donald Trump ya rattaba hannu kan sabuwar dokar da ta haramtawa wasu kasashen musulmi shida shiga Amurka na kwana 90.

A sabuwar dokar dai wadda za ta fara aiki a ranar 16 ga watan Maris, ta cire kasar Iraki daga cikin jerin kasashen.

Daya daga cikin abubuwan da dokar dai ta haramta sun hada da hana 'yan gudun hijra shiga Amurkar har zuwa kwana 120.

Wata kotun tarayya ce dai ta yi watsi da dokar ta farko wadda ta haddasa rudani a filin jiragen saman kasashe da dama.

Mene ne banbancin dokar farko da wannan?

Bisa sabuwar dokar dai har yanzu haramcin shiga Amurka na kwana 90 ga 'yan kasar Iran da Libya da Syria da Somaliya da Sudan da kuma Yemen yana nan daram.

Sai dai kuma an cire sunan Iraki daga jerin sunayen bisa dalilin da fadar White House ta bayar na cewa kasar ta inganta harkar bayar da bisa zuwa Amurkar.

Sabuwar dokar dai kuma ta amince da shigar 'yan gudun hijra cikin Amurka wadanda tun da farko ma'aikatar cikin gidan kasar ta yarje musu shiga.

Ta kuma dage haramcin da ta dora kan dukkannin 'yan gudun hijrar kasar Syria.