Facebook ya 'gaza' wajen hana wallafa hotunan lalata da yara

Secret group
Image caption Tun a bara ne BBC ta fara irin wannan bincike

An yi tir da shafin sada zumunta na Facebook kan yadda yake bari ana ta'ammali da kuma wallafa hotunan batsa na yara ko yada ake lalata da yaran a shafin.

Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar dokokin Birtaniya, Damian Collins, ya ce yana matukar tabbaba kan ko kamfanin na Facebook na yin garanbawul yada ya kamata kan abubuwan da suka shafi hakan don kawo gyara.

Kalaman na Mista Collins na zuwa ne bayan da BBC ta yi rahoto kan cewa Facebook bai cire kashi 80 cikin 100 na gomman hotunan batsar yara da ke shafin ba.

Hotunan sun hada da na shafukan mutane daban-daban inda maza ke tattauna yadda za su yi musayar hotuna ko bidiyo da ke nuna yadda ake lalata da yara.

Bayan da aka gabatar da misalan hotunan, sai Facebook ya yi karar wakilin BBC din da ya bayar da rahoton a wajen 'yan sanda, ya kuma soke hirar da ya shirya yi da BBC din.

Daga bisani kuma sai kamfanin ya fitar da sanarwa, inda ya ce: "Doka ba ta yarda da wallafa hotunan lalata da yara ba, yin hakan taka doka ne."

Mista Collins ya ce, "Ba a saba ganin lamarin da aka kai karar kafar yada labarai ta BBC ba don kawai tana kokarin kawo gyara a al'umma."

Image caption BBC ta bayar da rahoton gomman hotunan batsar yara ga kamfanin Facebook

A shafinsa na maraba da zuwa, kamfanin Facebook ya ce yana cire duk wani abu da ya shafi batsa.

Ya rubuta cewa, "Ba a yarda da duk wani abu da ya shafi batsa ko lalata ba a wannan shafin."

Kamfanin yana kuma karfafawa masu bin sa gwiwa cewa su danna wani maballi a shafin mai taken "report button", don ankarar da kamfanin duk wani abu da aka wallafa wanda bai dace ba.

Kamfanin dai ya ce ya inganta wannan mataki tun bayan wani bincike da BBC ta yi a bara.

Wanda ya gano wasu asirtattun shafuka da masu lalata da yara ke haduwa suna musayar hotuna.

Bayanin da BBC ta gabatarwa 'yan sanda a lokacin ya yi sanadin da aka daure wani mutum na tsawon shekara hudu a gidan kaso.

A kokarinta na gwada abin da Facebook ya ce, kafar yada labarai ta BBC ta yi amfani da maballin 'report button' don ankarar da kamfanin kan wasu hotuna 100 amma bai yi komai akai ba, wanda hakan ya nuna Facebook ya karya ka'idojinsa.

Sun hada da:

  • shafukan da na maza ne zalla masu sha'awar yin lalata da yara
  • hotunan yara 'yan kasa da shekara 16 a wani yanayi na bayyana tsiraici, inda ake sharhi a gefen su
  • akwai shafukan da aka sanyawa sunaye kamar "'yan shilan 'yan mata masu zafi, inda ake sato hotunan yara ake wallafawa
  • wani hoto da aka dauko daga cikin wani bidiyo da ke nuna yada ake lalata da yara, da kuma bukatar da aka sa a kasan hoton da ke cewa ana iya aikawa wasu hoton

Hotuna 18 kawai aka cire daga cikin 100 din da aka wallafa.

Amma a cewar Fcebook daga amsar da shafin ke bayarwa kai tsaye, ya nuna cewa sauran hotuna 82 din ba su kaucewa tsarinsa ba.

A dokar Facebook dai, mutanen da aka taba kamawa da laifin lalata ba za su iya bude shafi ba.

Kwayar cutar kwanputa ta 'kashe' shugaban Facebook

Amma sai gashi BBC ta gano wasu mutum biyar masu sha'awar lalata da yara da aka taba gurfanarwa a gaban shari'a, kuma aka ankarar da Facebook din ta shafin da ya bukaci a yi haka din. Sai dai bai dauki wani mataki a kansu ba.

Da yake mayar da martani, Mista Collins ya ce, "Wannan lamari ya dame ni matuka, kuma sam ba za a yarda da wannan abu da aka samu ba."

BBC ta kuma nuna sakamakon binciken nata ga kwamishinar kula da al'amuran yara ta Ingila, Anne Longfield.

Ta ce, "Na kadu matuka da abin da na gani, ban ji dadi ba ganin cewa shekara daya kenan da yin irin wannan binciken amma har yanzu ana wallafa irin wadannan hotuna a Facebook, sam ba za mu yarda da hakan ba," in ji ta.

Image caption Masu amfani da irin wadannan shafukan batsar suna kalamai marasa dadi ne kan yara

A karshen shekarar 2015 ne BBC ta bukaci yin hira da Facebook kan matakan da yake bi don magance irin wadannan matsaloli, kuma ta sake nanata wannan tambayar bayan sake binciken na baya-bayan nan.

Daraktan da ke kula da walwalar jama'a na kamfanin Simon Milner, ya amince zai tattauna da BBC a makon da ya gabata, da sharadin cewa BBC din za ta gabatar da misalai na irin wadannan hotuna da ta gano, amma kuma ba a cire su ba.

BBC ta yi hakan, sai dai kuma sai Facebook ya kai karar kafar yada labaran gaban hukumar kula da miyagun laifuka ta Birtaniya.

Mista Collins ya ce abin da kamfanin ya yi bai dace ba don kawai ana kokarin tabbatar da tsaftace abin da ke faruwa a shafin wajen cire duk abin da bai dace ba.

Image caption Tun a bara ne BBC ta fara irin wannan bincike

Wani daraktan BBC David Jordan, ya ce abin da Facebook din ya yi ya ba su mamaki kwarai.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba