Shin 'yan Nigeriaya na zuwa hutu kuwa?

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Najeriya sun nuna shakku a lokacin da mai magana da yawun shugaba Buhari ya ce Shugaban ya je hutu ne London

A jerin wasikunmu daga 'yan jaridar Afirka, Sola Odunfa ya duba dabi'ar 'yan Najeriya a kan zuwa hutu, a daidai lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya shafe wata guda don ya ga likita a Ingila.

Ko a ina ma dai aka kirkiri zuwa hutu a hukumance, tabbas ba daga Najeriya aka kirkire ta ba.

Lokacin hutu, lokaci ne da mutum ke daukar wasu kwanaki daga wurin aiki domin ya huta.

Lokaci ne dai mutum zai kara samun kuzarin komawa aiki.

Zai iya kasancewa lokaci da mutum zai iya blaguro zuwa wani wurin domin yawon bude ido.

An saba daukar hutun duk shekara kuma ya kan kai tsawon kwanaki ko ma makonni.

Amma ga dan Najeriya tsadar rayuwa ya sa ba shi da halin zuwa irin wannan hutun.

Ga masu hali kuma, idan har suka yi irin wannan tafiyar, ziyarar wurin adana kayan tarihin kasar ba ya gabansu.

Na sha zuwa irin wannan hutun.

Na kan dauki kaya kamar kala biyu na saka a kasan akwati na, sai kuma na karasa cika shi da kayan aiki na kamar kaset da abin nadar murya da lasifika da kuma littafi.

Sola Odunfa:

Image caption Ga masu hali kuma, idan har suka yi irin wannan tafiyar, yawon kallle-kalle abubuwan al'adun kasar da suka kai ziyara baya gabansu.

"Mu a wurinmu zuwa hutu shine bayan ka dawo, ka saya wa matarka ko burudurwaka kayan kawa da sabbin takalma da riguna kuma ka cika falonka da sabbin kayan laturoni"

Tabbas idan kana kasashen waje, sai kayi ta yawo zuwa gidajen cin abinci na Najeriya domin kwatanta farashinsu da na gida.

Sannan kuma akwai shaguna.

Na sha zuwa hutu Ingila amma, don Allah kar ka tambaye ni a kan fadar sarauniya ko gidan adana kayan tarihi na Burtaniyan.

A lokacin bazara da kuma gabanin kirisimeti, mutane na sayen akasarin kujerun kamfanonin jiragen sama.

Wannan ne lokacin da 'yan Najeriya da dama ke daukar hutunsu.

Matafiyan basa yin balaguro da kaya dayawa amma kuma aljihunsu a cike suke tafiya.

Kamar ni, zan iya tabbatar maka da ba tafiya za su yi domin suje kallon fadar sarauniyar Ingila ba ko Eifel Tower da ke Paris ko mutum-mutimi da ake kira statue of Liberty da ke Amurka.

Za su je sayayya ne kurun - kuma makudan kudi suke kashewa.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Najeriya da dama na zuwa London hutu ba tare da sun kai ziyara fadar sarauniya ba

Mu kan shafe 'yan kwanaki ba tare da munje sayayya ba.

A watanni biyu da suka gabata, 'yan Najeriya ba su damu ba da shugaba Muhammadu Buhari ya sanar cewar zai je hutu London.

'Yan uwanshi da abokai sunji dadin sanarwar.

Amma kuma 'yan Najeriya sun sauya tunani bayan da shugaban ya ce ya je ganin likitanshi ne.

Ta yiwu yana so ya dauki hutu ne daga tarin kiran wayoyin salula da ya ke amsawa a matsayinshi na shugaban domin ya kara samun sauki sosai.

Amma a ganinmu, a matsayinmu na 'yan kasa, mai magana da yawun shugaban ya yi yawo da hankalin mutane. Wa ke yin balaguro domin ya huta?

A tunaninmu, mutumin ya yi tafiya ne domin ganin likita kawai.

Labarai masu alaka