'Yan Masar na zanga-zanga kan burodi

Mai gasa burodi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Zanga-zangar ta yadu zuwa sassa daban-daban na kasar

Dubban mutane a sassa daban-daban na kasar Masar na zanga-zanga a kan tallafin da gwamnatin kasar ke basu na biredi.

An dai fara zanga-zangar ne a birinin Al-askandariya, inda masu gidajen gasa biredin suka shaidawa masu sayan, gwamnati ta rage yawan biredin da ake basu na kaso 6 zuwa kaso 1.

Masu gidajen biredi sun sanar da masu sayen cewa zasu bayar da biredin ne kawai idan har suna da kati.

Nan da nan zanga-zangar ta yadu zuwa sassa daban-daban na kasar ciki har fa babban birnin Masar wato Alkhahira.

A shekarar 1977 an yi wata zanga-zanga makamanciyar wannan a lokacin da shugaba Muhammad Anwar Sadat ya rage tallafin biredin da ake bai wa 'yan kasar.

Labarai masu alaka