An yi wa 'yan matan gidan marayu fyade a Indiya

An Indian social activist holds a placard during a protest against a rape at Hauz Khas village in New Delhi on February 21, 2017 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Laifukan fyade da na jinsi sun fito fili a Indiya

'Yan sanda a jihar Kerala ta kudancin Indiya sun kama mutum shida wadanda ake zargi da yi wa 'yan matan gidan marayu fyade a gundumar Wayanad.

'Yan sandan sun ce wasu mutane biyu sun ja hankalin yaran zuwa cikin wani shago ne kan cewa za su ba su alawar chakulet.

Sun ce mutanen sun nadi bidiyon fyaden kuma sun yi amfani da shi wajen tilasta wa 'yan matan su yarda su kara lalata da su.

Hukumomi sun bayyana lamarin a matsayin wani abu na jahilci kuma sun ce suna gudanar da bincike kan ko abin ya rutsa da wasu 'yan matan na dabam.

Inspekta TP Jacob yaa shaida wa wakilin BBC Ashraf Padana cewa : "Kuma muna yi wa mutanen tambayoyi domin gano in akwai wasu da ke da hannu a lamarin."

Wani mai magana da yawun gidan marayun wanda yake da kimanin yara 1,000, a ciki, ya ce ana bai wa yaran shawarwari.

Laifukan fyade da na jinsi sun fito fili a Indiya bayan wasu karti sun yi wa wata daliba fyade, suka kuma kashe ta a shekarar 2012 a birnin Delhi.

An kaddamar da dokokin hana fyade masu tsauri domin dakile matsalar. Amma duk da haka ana ci gaba da ba da rahotannin aikata laifin kan mata da yara a fadin kasar.

Karin bayani