'Ba za a hana 'yan Najeriya zuwa Amurka ba'

Donald Trump Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Donald Trump ya ce Musulmi ya sha alwashin kakkabe ta'addanci daga Amurka

Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja, babban birnin Najeriya ya fitar da wata sanarwa da ke karin haske kan takardar izinin shiga kasar.

Sanarwar ta ce yana so ya shaida wa 'yan Najeriya cewa babu wani dalili da zai sa wani dan Najeriya da ke da takardar izinin shiga Amurka ta ainihi ya dage ko ya soke tafiya zuwa kasar.

Wannan na zuwa ne bayan da a ranar Litinin wata jami'ar gwamnatin Najeriya ta bai wa 'yan kasarta shawarar kar su yi gaggawar tafiya Amurka bayan an hana 'yan Najeriya da dama wadanda ke da bizar damar shiga kasar.

Sanarwar Amurkan ta ce: "Ba a ambato sunan Najeriya ajerin sunayen kasashen da aka hana shiga Amurka a ranar 6 ga watan Maris ba. Ba a haramta zuwa Amurka ga 'yan Najeriya mazaunanta da kuma masu bisa ko wasu takardun da ke bada damar shiga kasar shigarta ba".

A ranar Litinin ne dai Abike Dabiri-Erewa, mai bai wa shugaban Najeriya shawarwari kan harkokin waje, ta ce a 'yan makonnin da suka gabata, an samu rahotannin 'yan Najeriya da ke da takardun shiga kasar na ainihi amma kuma aka hana su shiga kuma aka maido su nan take a jirgin da zai zo Najeriya kuma aka soke bisarsu.

Ta ce hukumomin aikin shige da fice na Amurka ba su bayar da dalilai na matakan da suk dauka ba.

Labarai masu alaka