Mutum 30 sun mutu a harin da aka kai asibitin Afghanistan

Jami'ai a kasar Afghanistan sun ce akalla mutum 30 ne suka mutu sakamakon wasu hare-hare da wasu mutane da suka yi shiga irin ta likitoci suka kai a babban asibitin soji da ke birnin Kabul.

Maharan, dauke da bindigogi da gurneti-gurneti, sun shiga cikin asibitin ne bayan daya daga cikin su ya tashi bam din da ke hannunsa a kofar shiga asibitin sannan ya bude wuta kan ma'aikata da marasa lafiya.

Sojojin kundumbalan da suka yi dirar-mikiya kan rufin kwanon asibitin na Sardar Daud sun kashe mahara hudu bayan sun kwashe sa'o'i da dama suna ba-ta-kashi.

Kungiyar IS ta yi ikirarin kai harin.

Amma kungiyar Taliban ta nesanta kanta da kai shi.

Ma'aikatar tsaron kasar ta ce an jikkata fiye da mutum 50.

Shugaba Ashraf Ghani ya ce harin da akai kai kan asibitin mai gado 400 ya "keta dukkan hakkokin dan adam".

Ya kara da cewa, "A kowanne addini, ana mutunta asibiti don haka kai masa hari tamkar kai wa dukkan kasar Afghanistan hari ne."

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Hayaki ya rika tashi daga rufin kwanon asibitin
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption An fitar da marasa lafiya daga asibitin
Hakkin mallakar hoto AFP/Getty
Image caption 'Yan sanda sun rufe hanyoyin da ke kai wa asibitin

Labarai masu alaka

Karin bayani