Za a binciki sojin Nigeria kan take hakkin ɗan adam

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin Najeriya sun ce sun yi nasarar fatattakar 'yan Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da wani kwamiti mai zaman kansa da zai gudanar da bincike kan zargin take hakkin dan dama da ake yi wa wasu sojojin kasar.

Babban Hafsan hafsoshin sojin kasar, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ne ya kaddamar da kwamitin ranar Laraba a Abuja, babban birnin tarayyar kasar.

Kakakin rundunar sojin kasa, Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka ya shaida wa BBC cewa, "Tun da shugabanmu babban hafsan hafsoshi ya kama aiki ya ce ba zai lamunci cin zarafin bil adama ba, shi ya sa muka bude ofishin da zai rika daukar mataki kan sojojin da aka samu da keta hakkin bil adama".

A cewarsa, kaddamar da kwamitin zai sanya wasu jami'ansu su rage azarɓaɓin da suke yi na cin mutuncin bil adama.

Sojojin na Najeriya dai sun yi kaurin suna wajen take hakkin dan adam, inda a lokuta da dama sukan far ma mutane kan laifukan da ba su taka kara sun karya ba.

Ko da a kwanakin baya, sai da rundunar sojin ta ladabtar da wasu jami'anta da suka ci zarafin wani gurgu saboda kawai ya sanya tufafin rawad-daji na sojoji.

Kzalika, Amurka da kungiyoyin kare hakkin dan adam irin su Amnesty international sun sha caccakar rundunar sojin ta Najeriya saboda zargin da suke yi mata da take hakkin dan adam a yakin da take yi da mayakan kungiyar Boko Haram da ma kungiyar da ke fafutikar kafa kasar Biafra, zargin da ta sha musantawa.

Labarai masu alaka