An tsare wasu mutane saboda 'zina' a Hadaddiyar Daular Larabawa

UAE Hakkin mallakar hoto CULVERWELL FAMILY
Image caption Emlyn Culverwell da Iryna Nohai sun hadu ne, a lokacin da yake aiki a UAE

An tsare wani da Afrika ta Kudu da wata 'yar Ukraine a Hadaddiyar Daular Larabawa saboda zarginsu da yin zina, inda za a yanke musu hukuncin shekaru da dama a gidan kaso idan har aka same su da laifi.

An kama Emlyn Culverwell, mai shekara 29 da Iryna Nohai mai shekara 27 ne,a lokacin da likita ya gano Ms Nohai da ke fama da ciwon ciki na da juna biyu.

An kama su da laifin zina.

Mahaifiyar Mista Culverwell ta roki da a sake su, inda ta ce "laifin da kawai suka yi shi ne na son junansu"

Ma'aikatar harkokin wajen Afrika ta Kudu ta ce ba za ta iya taimakon mutanen ba saboda wannan al'amari ne da ya shafi dokokin cikin gidan Hadaddiyar Daular Larabawa.

Wakiliyar BBC Pumza Fihlani da ke Johannesburg ta bayyana cewa gwamnatin Afirka ta Kudu ta ba su shawara su nemi lauya.

Har yanzu gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa bata mayar da martani kan batun ba.

Tun cikin watan Janairu ake tsare da Mista Culverwell da Ms Nohai, amma sai yanzu labarin ya yadu.

Mista Culverwell ya kwashe shekara biyar yana aiki a Hadaddiyar Daular Larabawar.

Mahaifiyarsa Linda, ta aike wa kamfanin yada labarai na News24 cewa suna kokarin aike musu sakonni domin su shaida musu cewa suna son su kuma kar su damu da halin d auke ciki.

Mrs Culverwell ta ce har yanzu ba a gurfanar da mutanen biyu ba, sai dai hukumomi na ci gaba da bincike.

Idan har aka kama su da laifi, za a iya yanke musu hukuncin shekaru da dama a gidan yari.

Labarai masu alaka