Bankunan Najeriya za su kwace kamfanin Etisalat

Tambarin etisalat Hakkin mallakar hoto Google
Image caption CBN da hukumar NCC na kokarin shawo kan lamarin

Wasu daga cikin bankunan Najeriya sun ce za su kwace ikon tafiyar da kamfanin wayar salula na Etisalat da ke kasar bayan ya kasa biyan bashin da ya karba a wurin su.

A ranar Alhamis ne dai Farfesa Umar Danbatta, shugaban hukumar da ke sa ido kan harkokin sadarwa da shugaban babban bankin Najeriya da tawagarsa suka gana kan batun.

Babban bankin Najeriya ne ya jagoranci ganawar da ya yi da NCC domin kara tattaunawa kan hanyar da tafi dacewa bankunan su janye yunkurin kwace ikon Etisalat.

Bayan ganawar ne dai suka yanke shawarar za su shiga tsakani kan bashin da ke tsakanin Etisalat da bankunan.

CBN ya amince ya gayyato shugabannin Etisalat din da bankunan da suka ba shi kudin domin su yi wata ganawar ranar Juma'a.

A farkon makon nan ne dai hukumar ta NCC ta dauki mataki inda ta nemi shawarar CBN, bayan da ta gano irin hadarin da kwace ikon kamfanin zai janyo wa harkokin sadarwar kasar.

Hukumar da ke sa ido kan harkokin sadarwa ta damu da halin da mutane sama da miliyan 20, wadanda ke amfani da Etisalat, za su shiga da kuma yadda lamarin zai shafi wadanda ke da niyyar sanya hannun jari a kamfanin.

Labarai masu alaka