Kwanan nan zan koma asibiti — Buhari

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Zan sadaukar da kaina wajen yi muku hidima — Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yana samun sauki sosai kan rashin lafiyar da ke damunsa, "amma watakila nan da makonni kadan masu zuwan zan koma asibiti".

Ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi wa 'yan kasar a fadarsa da ke Abuja jim kadan bayan saukarsa daga birnin London, inda ya kwashe kusan wata biyu yana hutu da kuma jinya.

A cewarsa, bai taba kwantawa rashin lafiya irin wacce yake fama da ita yanzu ba.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, "Ina matukar nuna godiya ga dukkan 'yan Najeriya, Musulmi da Kirista, wadanda suka yi ta yi min addu'a, kuma suke ci gaba da yi min addu'ar samun sauki".

Shugaban na Najeriya ya ce babban abin da zai sanya a gaba yanzu shi ne yi wa 'yan kasar aiki tukuru domin bayyana musu irin jin dadin da ya yi da addu'o'in da suka yi masa.

'Zan ci gaba da hutawa'

Muhammadu Buhari ya ce zai ci gaba da hutawa a gida kafin ya koma aiki.

Har yanzu babu cikakken bayani kan abin da ke damun shugaban amma jami'ansa sun nace cewa babu wani abin damuwa a cikin lamarin.

Shugaban ya isake cincirindon 'yan fadarsa wadanda suka tarbe shi lokacin da ya isa Abuja.

Wakilin BBC Haruna Tangaza ya ce ya ga ministocin shugaban da wasu gwamnoni da dama, "Dukkansu suna cikin walwala da farin ciki."


Kalubalen da ke gaban Buhari, Martin Patience, BBC Lagos

Hakkin mallakar hoto Nigerian Government
Image caption Shugaban ya gana da mataimakinsa da kuma wasu gwamnonin kasar da ministoci

Abu ne mai matukar muhimmanci ga shugaban kasar ya nuna wa 'yan kasa ya samu koshin lafiya da cikakken jagoranci a kwanaki kadan masu zuwa.

Idan ba haka ba, ba za a daina hasashen da ake akan cutar tasa ba, wacce ba a bayyana irin ta ba.

Abokan hamayyarsa na siyasa suna tambayar ko shugaban kasar ya samu lafiyar da zai ci gaba da jan al'amuran gwamnati.

Idan ya yi tafiyar hawainiya a wajen gudanar da ayyukansa to wannan zai kara musu kwarin gwiwar adawa.

Har ila yau za su kwatanta yadda mataimakinsa Yemi Osinbajo ya nuna kwarewa a matsayinsa na mukaddashin shugaban kasar a makonnin da suka gabata, inda tsarinsa ya sha bam-bam da na Shugaba Buhari.

Shugaban ya dawo, amma za a iya cewa ba lallai ne ya ci gaba da harkokinsa kamar yadda ya saba ba.


Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Da sanyin safiyar Juma'a ne Buhari ya isa Najeriya

A karshen jawabinsa, Shugaba Buhari ya ce "Dagangan na dawo a karshen mako saboda "mataimakin shugaban kasa ya ci gaba da lura da al'amura, ni kuma na ci gaba da hutawa".

A ranar Alhamis ce mai magana da yawun shugaban Femi Adeshina ya sanar da cewa Muhammadu Buhari zai koma gida.

Sanarwar da ya fitar ta ce shugaban ya gode wa ɗaukacin al'ummar Nijeriya da ma na kasashen waje kan addu'o'in da suka rika yi masa da fatan alkhairi.

A baya-bayan nan wayar da ya yi da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, lokacin da aka fara jin muryarsa tun bayan zuwa hutun jinyar, ya sa zuciyar 'yan ƙasar da dama kwanciya.

An yi ta ganin hotunan Muhammadu Buhari da wasu fitattun 'yan Nijeriya yayin ziyarar da suka riƙa kai masa lokacin da yake jinya a London.

Hakkin mallakar hoto Nigerian Government

Labarai masu alaka