Yadda rikicin Boko Haram ya naƙasa kasuwancin kifi a jihar Borno

Kasuwar kifi ta Tashar Baga a Maiduguri
Bayanan hoto,

Hana shigowa da kifin Maiduguri daga garin Baga ya haifar da karanci da kuma tsadarsa

Dubban masunta da dillalai a kasuwar kifi ta tashar Baga da ke Maiduguri ne, a jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya hare-haren Boko Haram suka yi wa mummunan tasiri.

'Yan kasuwar na kokawa da irin halin matsin da suka shiga, sakamakon hana shigo da kifin da jami'an tsaro suka yi daga garin Baga da ke kusa da tafkin Chadi, inda ake kamun kifin.

Hakan dai ya biyo bayan matsalar hare-haren Boko Haram a yankuna da dama na jihar Borno ciki har da Baga din, inda suke zargin mayakan na amfani da kasuwar kifin wajen samun kudaden shiga.

Kasuwar kifin ta tashar Baga dai ta shafe kusan shekara 40 ana hada-hadar kifin da a kan kama a yankin tafkin Chadi.

Ya kasuwar take ne kafin rikicin Boko Haram?

Kafin rikicin Boko Haram ya ƙara ƙazanta a shekara ta 2009, shahararriyar kasuwar kifin ta tashar Baga na samar da kuɗaɗen shiga ga mutane da dama, kama daga direbobi, da leburori, da matasa maza da mata.

Ta kasance wata cibiyar hada-hadar bandar kifin, inda dillalan kifi da masunta daga sassan ƙasar, da kuma wasu ƙasashe maƙwabta ke gudanar da harkokin kasuwancinsu.

A kan dai riƙa yin lodin kwalayen bussashen kifin a manya-manyan motoci ana safarar su zuwa wasu jihohin kudancin ƙasar da ma babban birnin tarayya Abuja.

Kasuwar dai wacce ke cikin birnin Maiduguri ta samu sunanta ne daga garin Baga wanda ke da nisan kilomita 196 daga birnin.

A lokacin da wakiliyar BBC Bilkisu Babangida ta ziyarci kasuwar kifin, ta ganewa idonta irin koma bayan da aka samu a harkokin kasuwancin, ba kamar a shekarun baya ba a lokacin take garin.

Alhaji Ahmadu Na A'i, wanda shi ne sakataren kudi na kungiyar masu kamun kifi da sarrafawa, ya shaidawa BBC cewa da ko da yaushe aka zo nan za ka ga kifi a tattare ga masu saye Yarbawa da 'yan kabilar Ibo da sauransu, daga sassa daban-daban na Najeriya''.

Ya kuma ce, ''Matsalar Boko Haram ce ta shafi kasuwancin kifin yanzu duk a takure muke.''

Bayanan hoto,

Baya ga kifi a wannan kasuwa har ma ana sayar da naman daji da aka fi sani da 'Bush Meat'

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Baya da kifin dai da aka san wannan kasuwa da shi, akwai kuma masu sayar da naman daji da aka fi sani da 'Bush Meat,' da suma ake kai wa wasu kasashe da wasu sassan kasar.

Sani Masta, daya daga cikin masu sayar da naman dajin ya shaidawa BBC cewa, manyan mutane daga sassan jihohin Benue da Lagos da Nassarawa da su Otukpor na zuwa saye, amma yanzu ya ce kasuwancin ya ja baya sosai.

Ya ce, ''Yanzu wannan teburin da ki ke gani na hadin guiwa ne, a baya kuma mutum daya ne ke da teburi daya.''

Akwai kuma bangaren bandar naman shanu da wani dan kasuwa Auwal Mohammed ya shaida wa BBC cewa idan sun kasa a jeji sai a yanka a yi bandar su.

''Ana dura shi a buhu ne, bandir-bandir, kwayar dari da sittin shi ne bandir daya,'' a cewarsa.

A lokacin da take tashe, shaharariyar kasuwar kifi ta tashar Baga da ke birnin Maiduguri na alfahari da kasancewa kasuwar kifi mafi girma a Afirka.

Amma kuma hare-haren Boko Haram a cikin shekara bakwai sun haifar da koma bayan al'amura, tare da kasancewa wuri mai hadari ga masu saye da sayarwa da ke hada-hada cikin zaman dar-dar.

A wannan kasuwar kifi akwai masu sayar da kayan kamun kifi, matuka jiragen ruwa da suka dawo cikin garin Maiduguri suna zaman jiran tsammani, galibinsu 'yan kudancin Najeriya ne.

Mista Uchenna, shi ne sakataren kungiyar masu sayar da kayan kamun kifin a jihar Borno, ya kuma ce yanzu halin da suke ciki babu dadi saboda babu kasuwa.

Ya ce, ''Yanzu akwai kaya amma babu masu saya, muna zaman kashe wando, da muna samu mu ci mu sha har mu ba almajirai, amma yanzu ko na almajiran ma zan iya karba saboda komai ya tsaya.''

Bayanan hoto,

Galibin 'yan kasuwar kifin musamman matasa na zaman kashe wando ne

Hana shigo da kifi cikin Maiduguri daga garin Baga shi yafi damun 'yan kasuwar

Yanzu dai babbar matsalar 'yan kasuwar ita ce rashin bude hanyar shigowa da kifin daga garin Baga zuwa Maiduguri don su ci gaba da kasuwancinsu.

Hakan ya sa kifin ya kara tsada saboda ba a samun sa kamar yadda ya kamata.

Malam Jibrin wani mai sayar da kifi, ya shaida wa BBC cewa kasuwa babu dadi saboda kifi ya kan dade bai zo ba, kuma mutane babu kudi a hannunsu, kuma sannan kifin ma ya yi karanci.

Ya ce, ''Yanzu sai kazo kasuwar ma ya kai sau nawa ka tashi ba ka samu komai ba, wannan kwalin kifin da ki ke gani muna sayar da shi dubu biyar zuwa shida, a da kuwa bai wuce dubu biyu ba.''

Hon Haruna Kukawa dan majalisar tarayya ne daga yankin na Kukawa inga garin na Baga yake, ya ce, ''Gaskiya ne yanzu an hana shigowa da kifi da dabbobi ma saboda matsalolin tsaro."

Ya ce, ''Mun sha zama da su kungiyar masu sayar da kifin da sojojin na Baga da na Monguno da gwaman jihar Borno, har mun sa shuganannin kungiyar sun samu babban hafsan sojin Najeriya Janar Buratai, amma ya ce abin sai a hakali.''

Bayanan hoto,

Mata ma saurin samun mazajen aure a kasuwar kifin a baya can saboda akwai harkar kudi

A baya dai mata na saurin samun mijin aure a kasuwar kifin ta tashar Baga

Sakamakon rikicin Boko Haram yanzu da dama yan kasuwar kifin na zaman kashe wando ne saboda harkokin sun ja baya.

In ji Mohammed Auwal wani magidanci ya ce da lokacin ana zaman lafiya a kullum daga Litini zuwa Jumma'a ana lodin manyan motocin sama da dari na kifi zalla.

Ya kuma ce ''Da din nan duk matar da bata samu miji ba in tazo kasuwar kifi za ta samu miji saboda akwai kasuwa akwai kudi, 'yan kasuwar suna yawan kara aure''

Hare haren Boko Haram sun yi mummunan tasiri kan kasuwancin kifia Borno

Kafin sojojin Najeriya su fatattaki mayakan na Boko Haram daga cikin birnin Maiduguri a shekara ta 2013, wuraren da suka fi kai manyan hare hare sune kasuwanni.

Su kan kai farmaki kasuwanni da rana tsaka tare da kwace wa jama'a kudade a bakin bindiga.

Kasuwar tashar Baga dake birnin na Maiduguri na daya daga cikin kasawannin da suka sha fama da hare-haren na Boko Haram.

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Kasuwar kifin ta tashar Baga ta sha fama da hare-haren kunar bakin wake na Boko Haram

A shekara ta 2011, akwai ranar da masu tayar da kayar bayan na Boko Haram suka dasa bama-bamai wajen biyar a kasuwar ta tashar Baga wadanda suka yi sanadin rayukan mutane da dama.

A ranar 22 ga watan Yunin shekara ta 2014 , wasu mata 'yan harin kunar bakin wake sun shiga cikin kasuwar suka tarwatsa kansu a kusa da wani masallacin da ke cikin kasuwar, lokacin ana sallar la'asar, inda suka hallaka mutum sama da 30 tare da jikkata da dama.

Kana a ranar 7 ga watan Maris na shekara ta 2015, wani dan harin kunar bakin wake a cikin babur mai kafa uku da aka fi sani da Keke NAPEP ya tayar da bam a kusa da kasuwar, tare da hallaka mutane da dama akasari masu sayar da kaya ne a bakin hanya da masu wucewa.

'Ba zan taba mantawa da wannan rana ba'

Alhaji Ahmadu na A'i, sakataren kudi na kungiyar masu kama kifi da sarrafawa a jihar Borno ya bayyana halin da suka shiga a wannan lokaci da cewa matsanaci.

Ya ce, ''Akwai wani abu da ba zan taba mantawa da shi ba game da irin hare-haren da ake kai musu a cikin kasuwar. Ya ce, ''Matasan mu na kasuwa su suka fara kama Boko Haram da hannWata rana wata Alhamis ba zan manta ba wani dan Boko Haram ya shigo cikin kasuwar ya harbi wani dan kabilar Ibo ya kwace

Malam Abubakar Umar matukin jirgin ruwa ne da ya dade a kan tafkin Chadi da yanzu haka ya kaura zuwa Maiduguri da ya ce ada yana da jiragen ruwa uku, amma yanzu babu ko guda daya, yanzu babu abinda yake yi sai tsince-tsncen kifi a wannan kasuwa.

Ya kuma ce '' Boko Haram sun kashe dan'uwana, yankan rago suka yi masa, kana sun kashe direbobina uku''

Dillan kifin daga kudancin Najeriya yanzu basu da wani karsashin yin kasuwanci saboda hare-haren Boko Haram, yawancinsu sun kauara zuwa garuruwansu na asali.

Haka suma masuntan dake zaune a yankunan Baga, Kukawa, Monguno, Mallam Fatori, Damasak da sauran wuraren dake kan tafkin Chadi da kogunan da sukan yi amfani da su wajen samun ababan more rayuwa akasari sun koma cikin Maiduguri, wasu kuma sun koma garuruwansu kamar su Kano, da Sokoto, da Kebbi, da Zamfara, da Naija.

Ko shakka babu da zarar hukumomin sun kara inganta tsaron a yankin tafkin Chadi, tare da sake bude hanyar shigo da kifin, tattalin arzikin yankin zai kara bunkasa fiye da yadda aka sani a da.

Garin Baga

Baga gari ne a arewacin jihar Borno da ke kusa da tafkin Chadi, a yankin karamar hukumar Kukawa, kuma cibiya ce ta hada-hadar kamun kifi da cinikayyarsa tun a shekara ta 1960, amma janyewar da tafkin ya rika yi sakamon sauyin yanayi ya fara janyo tabarbarewar al'amura.

Garin na da nisan kilomita 196 daga Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Akwai kuma babbar kasuwar kifi ta "Doron Baga" wacce ke da nisan kilomita shida daga garin na Baga, daga can ne ake yin bandar kifin bayan an kama, sannan a yi safararsa zuwa kasuwar tashar Baga ta Maiduguri.

A cikin watan Janairun shekara ta 2015 ne, mayakan Boko Haram suka sake kai babban farmaki garin na Baga suka kuma kwace ikonsa da ma wani sansanin sojin hadin guiwar kasashen Najeriya, da Nijar da Chadi ke amfani da shi domin fafatawa da mayakan.

Mayakan sun kaddamar da munanan hare-hare, tare da yi wa dubban mutane kisan gilla--mafi muni da aka taba samu a tarihin hare-haren Boko Haram.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun tsere zuwa kasashen Chadi da Nijar, yayin da wasu suka gudu cikin birnin Maiduguri.