Kun san abin da Buhari ya gaya wa 'yan Nigeria bayan dawowarsa?

Buhari da Osinbajo Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Buhari ya yaba wa mataimakinsa Osinbajo kan yadda ya tafiyar da kasar da baya nan

Jim kadan bayan dawowar shugaba Buhari daga hutun jinya a London, ya gana da ministocinsa da gwamnoni inda har ya gabatarwa 'yan Nigeria gajeren jawabi.

A cikin jawabin shugaba Buhari ya bayyana yadda likitoci suka duba shi, da abubuwan da aka yi masa, da irin ci gaban da ya gani a wannan fanni.

Ya kuma yabi mataimakinsa kan irin yadda ya rike kasar da baya nan.

Ga dai fassarar wani bangare daga jawabin nasa da ya gabatar a fadar gwamnati da safiyar Juma'a.

"Mai girma mataimakin Shugaban kasa, Masu girma gwamnoni da suke tare da mu a nan,Shugaban Jam'iyyar APC ta kasa, wato Oga kwata-kwata, Majalisar ministoci, Shugabannin rundunonin Soji, Shugaban 'yan sanda,'Yan Jarida, maza da mata, wannan dan gajeren jawabin na dauke da bangarori guda biyu

Na farko a kan batun kasa ne baki daya, don haka muna so 'yan jarida su lura da batun nan sosai.

Na biyu shi ne, akwai abubuwan da muka gani cikin watanni 18 din da muka yi a mulki, amma ni da mataimakina ne kawai muka san su.

Ina matukar godiya ga 'yan Najeriya, Musulmai da Kiristoci wadanda suka yi ta yi mana addu'o'i kuma suke ci gaba da yi mana addu'o'n samun lafiya.

Wannan alamu ne na kauna, duk da cewar an shiga wani mawuyacin hali, to 'yan Najeriya na ci gaba da goyon bayan gwamnatia kokarin ta na magance matsalolinmu.

Abin da ya kamata in yi in biya ku da shi, shi ne in kara sadaukar da kaina wajen yi muku aiki, da kare muradunku, da rike amanarku.

Na gode sosai, sosai. A yanzu ina samun sauki sosai yanzu, kuma watakila zan koma asibiti nan da 'yan makonni masu zuwa.

A maimakon turo da wakilai Abuja domin yi min maraba, zan fi so 'yan Najeriya su ci-gaba da yiaddu'o'i domin hadin kan kasarmu tare da ci-gabanta.

Na gode sosai sosai. Allah ya yi wa Kasarmu Albarka.

A lokacin da kirsimeti ta gabato na fada wa mataimakina, wanda na san yana da Coci, don haka yana bukatar zuwa gida.Sai na ce masa, za ka tafi hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara don haka idan ka dawo ni ma ni ma zan tafi nawa hutun, sai ya ce to.

Ina tsammanin bai je gida ba, kawai ya tafi wani waje ne ya labe.Don haka da ya dawo, sai na ce masa to ni ma fa yanzu lokaci na zai zo a 'yan watanni masu zuwa.

Daman kuwa shi ma yana da kwatankwacin manufofina, kuma ni ina jin wata 'yar gajiya a jikina kasancewa nayi aiki kusan watanni 18 don haka ina bukatar hutu.

Amma koma dai mene ne,ina gode wa 'yan Najeriya, bisa yabo da muke samu daga gare su, hakika ina sane da hakan, kuma ina matukar godiya da wannan.

Ina sane sosai da halin da tattalin arzikin kasa yake ciki, kuma na huta sosai kamar yadda ake bukata, kuma na samu kulawar da ta dace duk wani dan Adam ya samu.

Ba zan tuna lokacin da na taba yin rashin lafiya irin wannanba, tun lokacin da nake sauyari har ma lokacin da nake cikin fadi-tashin aikin soji.

Amma kuma na fahimci cewa ana samun ci gaban fasahar zamani sosai, kuma na fahimci cewa mu, idan na ce "mu" ina nufin gwamnati da jama'a baki-daya ya kamata mu rungumi fasahar zamani .

Saboda bazan iya tuna lokacin da aka yi min karin jini ba.Ba zan iya tunawa ba gaskiya, bazan iya tunawa ba cikin shekaru na 70 da na yi a duniya.

Kuma ba zan iya tuna lokacin da na samu magani mai karfi sosai irin haka ba, wanda 'yan Najeriya suke shan sa fiye da ka'ida..

Ina ga babbar matsalarmu ita ce rashin tsari wajen shan magani, ba ma bin dokar likita.

Saboda a wuraren da na ziyarta mutane sukan sha magani ne kawai,idan akwai bukatar hakan. Basa hadiyar magani ba a kan tsari ba kamar 'yan kasarmu.

To na dawo kuma ina farin cikin hakan, na yi farin cikin yadda mataimakinaya ji dadin rikon kwaryar da kuma aikin da ya yi tukuru. Kuruciyar sa da kaifin basirarsa sun taimaka masa wajen yin nasarar rikon.

Yayin da ni kuma yawan shekaru da kwarewar aikin soja ne suke taimaka min.

An saka dariya

Hakkin mallakar hoto Bashir Ahmad Twitter
Image caption Iyalansa sun tarbe shi

To da fatan 'yan Najeriya za su cigaba da ayyukanku na yau da kullum, Najeriya kuma za ta ci gaba ko muna nan ko bama nan.

Kuma shawara ta guda daya mai muhimmanci gareku ita ce, ku dauki Ilimin kowa da ke karkashinku da matukar muhimmanci. Na 'ya'yanmu da na 'yan uwanmu da kuma na mazabunmu.

Ilimi,Ilimi,Ilimi kamar yadda wani Firai ministan Birtaniya ya taba fada.Dole mu yi duk abi da za mu iya akan Ilimi.

Ina sane na dawo a karshen mako don mataimakin shugaban kasa ya ci gaba da aiki, ni kuma na cigaba da hutawa.

Na gode, Na gode sosai."

Jinya a London

Shugaba Buhari ya shafe kusan wata biyu yana hutun jinya a London, al'amarin da ya yi ta jawo ce-ce-ku-ce a kasar.

Sai dai an yi ta ganin hotunan Muhammadu Buhari da wasu fitattun 'yan Nijeriya yayin ziyarar da suka riƙa kai masa lokacin da yake jinya a London.

A ranar Alhamis ce mai magana da yawun shugaban Femi Adeshina, ya sanar da cewa Muhammadu Buhari zai koma gida.

Labarai masu alaka