Kwalara ta kashe mutum 200 a Somaliya

Wata mai fama da tamowa Hakkin mallakar hoto Save The children
Image caption Wata yarinya yar sama da shekara daya dake fama da tamowa da wasu cututtukan da suka danganci hakan

A wani gargadi da kungiyar bayar da agaji ta Save the Children ta bayar, ta ce barkewar cutar amai da gudawa a Somaliya ya kai wani mataki na tashin hankali da ke bukatar agaji domin shawo kansa.

Save da Children ta ce a kalla mutum 200 ne suka mutu daga mutane 8,400 da aka tabbatar sun kamu da cutar a wannan shekarar.

Somaliya dai na fama da matsanancin fari wanda ya jawo tabarbarewar al'amarin.

An kuma samu yara masu fama da cutar sanyin hakarkari a asibitoci 72 a lardin Puntland.

Jami'an kungiyar sun ce wahalar da ake sha yanzu ta fi ta wacce aka fuskanta a irin wannan loakcin a shekarar 2011, kafin a ayyana yankin a matsayin wanda ke fama da matsananciyar yunwa.

A kalla mutum miliyan 6.2 na bukar agajin gaggawa a cewar kungiyar.

Ta bukaci agajin dala miliyan 824 domin hana "matsalar zama gagaruma".

Labarai masu alaka