Golan Man City ya ce an mayar da shi cikon benchi

Joe Hart Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Joe Hart ya buga wa City wasa 348

Golan Manchester City Joe Hart ya ce an mayar da shi cikon benchi a kulob din kuma yana ganin ba za a sake sanya shi a gasar Premier ta Ingila ba.

A watan Agusta ne Hart ya koma kulob din Torino na kasar Italiya a matsayin aro bayan kocin City Pep Guardiola ya shaida masa cewa yana iya barin kulob din.

Dan wasan mai shekarar 29 ya kara da cewa da ma ya dade da sanin cewa Guardiola zai ki sanya shi a wasa.

Ya ce "Ban ga dalilin yin fada ba idan mutum ya san ba zai yi nasara ba musamman idan wanda za ka yi fada da shi ya fi ka sauri."

Amma Hart ya yi ammana cewa matakin da aka dauka da shi ba na "kashin kai ba ne" yana mai cewa ya mutunta matakin da Guardiola ya dauka.

Ya shaida wa BBC cewa "Bai dauki wannan matakin domin ya kawo cikas a rayuwata ba, ya dauke shi ne saboda yana ganin abin da ya yi shi ne daidai a matsayinsa na koci."

Da aka tambaye Guardiola a game da matsayin dan wasan a wani taron manema labarai da ya gudanar ranar Juma'a, ya jaddada matsayinsa cewa bai dauki mataki a kan Hart ba.

Labarai masu alaka