Jam'iyyar PDP ta yi wa Buhari barka da zuwa

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Zan sadaukar da kaina wajen yi muku hidima — Buhari

Jam'iyyar PDP da ke hamayya a Najeriya ta yi wa shugaban kasar Muhammadu Buhari barka da dawowa gida daga jinyar da ya yi a Ingila.

Wata sanarwa da PDP bangaren Sanata Ahmed Makarfi suka fitar, ta yi addu'ar Allah ya kara wa shugaban kasar sauki a kan cutar da yake fama da ita.

Ta ce: "Muna yi wa shugaban kasa addu'ar samun cikakkiyar lafiya sannan muna bayar da shawara ga fadar shugaban kasa cewa nan gaba ta daina boye-boye kan rashin lafiyar ta Shugaba Muhammadu Buhari".

PDP ta yi kira ga 'yan kasar su ci gaba da yi wa shugaban addu'a domin samun sauki cikin hanzari, sannan ta yaba wa mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo bisa rawar da ya taka bayan tafiyar shugaban jinya.

"Muna yin godiya ga mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo kan rikon da ya yi wa mulkin kasar nan a lokacin da shugaba ba ya nan.

Kakakin PDP Prince Dayo Adeyeye ya kara da cewa "muna kira a gare shi ya ci gaba da aikin da yake yi na fitar da kasar nan daga matsanancin halin tattalin arzikin da ta fada a ciki."

'Zan koma asibiti'

Shugaba Buhari dai ya ce yana samun sauki sosai, amma watakila nan da makonni kadan masu "ya koma asibiti".

Ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi wa 'yan kasar a fadarsa da ke Abuja jim kadan bayan saukarsa daga birnin London.

A cewarsa, bai taba kwantawa rashin lafiya irin wacce yake fama da ita yanzu ba.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, "Ina matukar nuna godiya ga dukkan 'yan Najeriya, Musulmi da Kirista, wadanda suka yi ta yi min addu'a, kuma suke ci gaba da yi min addu'ar samun sauki".

Shugaban na Najeriya ya ce babban abin da zai sanya a gaba yanzu shi ne yi wa 'yan kasar aiki tukuru domin bayyana musu irin jin dadin da ya yi da addu'o'in da suka yi masa.

'Zan ci gaba da hutawa'

Muhammadu Buhari ya ce zai ci gaba da hutawa a gida kafin ya koma aiki ranar Litinin.

Har yanzu babu cikakken bayani kan abin da ke damun shugaban amma jami'ansa sun nace cewa babu wani abin damuwa a cikin lamarin.


Kalubalen da ke gaban Buhari, Martin Patience, BBC Lagos

Hakkin mallakar hoto Nigerian Government
Image caption Shugaban ya gana da mataimakinsa da kuma wasu gwamnonin kasar da ministoci

Abu ne mai matukar muhimmanci ga shugaban kasar ya nuna wa 'yan kasa ya samu koshin lafiya da cikakken jagoranci a kwanaki kadan masu zuwa.

Idan ba haka ba, ba za a daina hasashen da ake akan cutar tasa ba, wacce ba a bayyana irin ta ba.

Abokan hamayyarsa na siyasa suna tambayar ko shugaban kasar ya samu lafiyar da zai ci gaba da jan al'amuran gwamnati.

Idan ya yi tafiyar hawainiya a wajen gudanar da ayyukansa to wannan zai kara musu kwarin gwiwar adawa.

Har ila yau za su kwatanta yadda mataimakinsa Yemi Osinbajo ya nuna kwarewa a matsayinsa na mukaddashin shugaban kasar a makonnin da suka gabata, inda tsarinsa ya sha bam-bam da na Shugaba Buhari.

Shugaban ya dawo, amma za a iya cewa ba lallai ne ya ci gaba da harkokinsa kamar yadda ya saba ba.


Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Da sanyin safiyar Juma'a ne Buhari ya isa Najeriya

A karshen jawabinsa, Shugaba Buhari ya ce "Dagangan na dawo a karshen mako saboda "mataimakin shugaban kasa ya ci gaba da lura da al'amura, ni kuma na ci gaba da hutawa".

A ranar Alhamis ce mai magana da yawun shugaban Femi Adeshina ya sanar da cewa Muhammadu Buhari zai koma gida.

Sanarwar da ya fitar ta ce shugaban ya gode wa ɗaukacin al'ummar Nijeriya da ma na kasashen waje kan addu'o'in da suka rika yi masa da fatan alkhairi.

A baya-bayan nan wayar da ya yi da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, lokacin da aka fara jin muryarsa tun bayan zuwa hutun jinyar, ya sa zuciyar 'yan ƙasar da dama kwanciya.

An yi ta ganin hotunan Muhammadu Buhari da wasu fitattun 'yan Nijeriya yayin ziyarar da suka riƙa kai masa lokacin da yake jinya a London.

Hakkin mallakar hoto Nigerian Government

Labarai masu alaka