Duniya na fuskantar bala'in da ba ta taba fada wa ba tun 1945

five-year-old Mohannad Ali lies on a hospital bed in Abs, Yemen Hakkin mallakar hoto Unicef
Image caption An kai wannan yaron dan shekara biyar mai suna Mohannad Ali wani asibitin Yemen saboda matsananciyar yunwa

Majalisar dinkin duniya ta ce duniya na fuskantar babban bala'in yunwar da rabon ta da fuskantar irin sa tun shekarar 1945, tana mai roko a dauki matakan kauce masa.

Babban jami'in bayar da agaji na majalisar Stephen O'Brien ya ce fiye da mutum miliyan 20 ne ke fuskantar bala'in yunwa da fari a Yemen, Somalia, Sudan ta Kud da Nigeria.

Tuni dai hukumar kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya, Unicef ta yi gargadin cewa yara 1.4m ka iya mutuwa sakamakon yunwa a wannan shekarar.

Mr O'Brien ya ce ana bukatar $4.4bn zuwa watan Yuli domin kauce wa wannan bala'i.

Ya shaida wa kwamitin tsaro na majalisar cewa,"Muna tsaka mai wuya. Ga shi muna farkon shekara amma tuni mun fara fuskantar bali'in yunwar da rabon mu da ganin rin sa tun da aka kirkiri majalisar nan."A cewar Mr O'Brien "Kananan yara sun tsimbire sannan ba sa zuwa makaranta. Rayuwarsu na cikin bala'i. Hakurin da jama'a ke yi na neman karewa. Mutane da dama za su rasa muhallansu sanna za su ci gaba da neman yadda za su rayu, lamarin da zai kawo tashin hankali a yankunan."


Labarai masu alaka