BH ta durkusar da 'yan kasuwar Monday Market a Maiduguri

Kasuwar Monday Market Maiduguri
Bayanan hoto,

Kwanciyar hankalin da aka samu a birnin Maiduguri ya sa 'yan kasuwar ci gaba da hada-hada

Kasuwar Litinin ta Maiduguri da aka fi sani da Monday Market tana daga cikin wuraren da suka sha fama da hare-haren Boko Haram, wadanda suka yi mummunan tasiri ga harkar kasuwanci.

Kasuwar dai ta kasance wata babbar cibiyar kasuwanci ce yankin arewa-maso-gabashin Najeriya, da aka saba hada-hadar kasuwancin kasa da kasa.

Dubban masu sayen kayayyaki ne daga sassan kasar da wasu kasashe makwabta kan zo kasuwar ta Monday Market don yin hada-hada.

Da yawa daga cikin 'yan kasuwan sun samu karayar arziki, amma kuma suna cike da fatan samun waraka, bayan da aka samu kwanciyar hankali a birnin.

A yayin wata ziyarar da tawagar BBC ta kai Jihar Bornon a kwanakin baya, Bilkisu Babangida ta ziyarci kasuwar ta Monday Market inda ta zagaya tare da tattaunawa da wasu daga cikin 'yan kasuwar kan yaddda al'amura ke tafiya.

Bayanan hoto,

Yawancin 'yan kasuwar sun samu karayar arziki saboda hare-haren Boko Haram

Alhaji Muhamamdu Adamu Mai Gilas daya daga cikin wadanda ke kasuwanci a bakin kasuwar ne wanda ya shaidawa BBC cewa yanzu al'amura sun daidaita da yake an samu zaman lafiya a cikin birnin, mutane sun fara shigowa sayen kaya, "amma kuma sun shiga tashin hankali a baya".

Amma ya ce sun sha fama a baya "Kin ga kamar a baya bakin shagona din nan za ki ga mutane fiye da hamshin son zo sun fake saboda harbe-harbe, idan kika duba bangon nan duk abubuwan tashin bama bamai ne, duka kofofin nan sai da muka sake sabbi,'' in ji shi.

Alhaji Adamu Jibrin na gudanar da kasuwancin tayoyi da karafunan tayar mota, ya ce duk da an samu zaman lafiya, amma kuma rashin zuwan mutanen da suka saba sayen kayansu daga kasashe makwabta ya haifar da cikas.

Hakazalika, Alhaji Kyari Mohammed shugaban kungiyar 'yan kasuwan Monday Market kokawa yake yi kan rashin jarin tafiyar da kasuwancinsu.

Ya ce "yawancinmu 'yan kasuwa mun samu karayar arziki, gwamnati dai ta yi alkawarin za ta bamu tallafin rance, muna nan muna jira''

Har ila yau, ya kara da cewa ''Boko Haram sun jefa mu cikin wani hali, galibi wasu ''yan kasuwar sun rufe shagunansu saboda karayar arziki."

Bayanan hoto,

Maman Chukudi 'yar asalin jihar Abia ce a kudancin Najeriya da ke da shago a kasuwar

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Kasuwar Monday Market wacce ke karkashin gwamnatin jihar Borno, ta kasance kan gaba wajen samar da kudaden shiga ga gwamnatin.

Amma kuma saboda yawan kai hare-haren da Boko Haram ke yi a kasuwar mahukuntan sun fuskanci koma baya wajen samun kudaden shigar saboda kaura da 'yan kasuwa suka rika yi musamman ma wadanda suka fito daga kudancin Najeriya, da kuma wasu kasashe kamar Chadi da Nijar da Kamaru da Jamhuriyar tsakiyar Afirka.

Maman Chukudi ta 'yar asalin jihar Abia a kudancin Najeriya ce dake sayar da kifi, da man ja da sauran kayan miya irin na 'yan kudancin kasar da ta shaidawa BBC cewa kasuwa yanzu dai sai hakuri da yake dai an samu kwanciyar hankali akwai karfin gwiwa.

Ta kuma kara cewa ''Farsashin kayan ya tashi, wannan kifin a watan Nuwamba na sayi buhunsa Naira dubu 43, amma yanzu ya kai dubu 50''

Hare-haren Boko Haram sun mayar da hannun agogo baya a kasuwar

A cikin watan Agustan shekarar 2010 ne al'amura suka fara sauya wa lokacin da wasu yan Boko Haram suka bindige wani jami'in dan sanda da ke bakin aiki a wajen kasuwar.

Tun daga shekarar 2010 zuwa 2013 kadai kasuwar ta shaida hare-haren kungiyar Boko Haram har sau 13.

Mayakan na Boko Haram sun kara zafafa kai hare-harensu ya zuwa na dasa bama-bamai da kunar bakin wake, da ya haddasa mutuwar daruruwan mutane da suka hada da yan kasuwa, da jami'an tsaro da masu sayayya.

Bayanan hoto,

Hare-haren Boko Haram sun mayar da hannun agogo baya a kasuwar Monday Market da ke Maiduguri

Domin shawo kan wannan matsala da kuma kare rayukan 'yan kasuwa ne hukumomi suka dau matakan tsaro a shekarar 2013 wajen daukar samari 'yan kato da gora don kara wa kan jami'an tsaro 55.

'Yan kato da gora fiye da dari ne aka dauka aikin, don gadin manyan hanyoyi hudu na zuwa wannan kasuwa, kamar hanyar Gwange, Gidan Madara, sha-tale-talen Tobacco da kuma titin Ahmadu Bello.

Hukumomin kasuwar kuma sun kara tsaurara matakan tsaro a manyan kofofi shida na shiga kasuwar, tare da girke jami'an soji da na farin kaya.

Su kan yi wa 'yan kasuwa da masu sayayya binciken kwakwaf kafin su shiga.

Amma kuma duk da irin wadannan matakai, masu kai harin kunar bakin wake akasari mata kan kutsa cikin kasuwa suna ta da bama-bamai tare da hallaka mutane da dama.

A watan Yulin shekarar 2014 ne kasuwar Monday Market ta shaida hari mafi muni a lokacin da wani dan harin kunar bakin wake ya tarwatsa kansa tare da hallaka mutane fiye da hamsin da kuma jikkata wasu 69.