Za ka so shiga caji ofis ɗin da ya fi otel tsada?

North Wales Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana kula da dakunan tsare mutanen sannan ba a ma cika samun masu laifin da za a tsare a ciki ba

Ana rufe wani caji ofis a Gwynedd da ke Wales ta arewa a Burtaniya bayan ta bayyana cewa kuɗin da ake kashewa wajen tsare mutum ya fi na otel ɗin ƙasaita tsada.

An kiyasta kuɗin tsare mutum a caji ofis ɗin Dolgellau a kan fam 623 a kowanne dare, yayin da kuɗin ɗaki a wani fitaccen otel ɗin London wato Savoy Hotel ya fara daga fam 464.

Rufe caji ofis ɗin zai tattalawa rundunar 'yan sandan North Wales fam dubu 300 duk shekara.

An gano cewa ba a cikakken amfani da ɗakunan tsare mutanen a caji ofis ɗin, inda aƙalla-akasara bai fi a tsare mutum ɗaya a kullum ba, kuma rabinsu ba sa wuce sa'a shida a ciki.

Sakamakon haka sai kuɗin tsare fursuna a Dolgellau ya ninka sau biyu, idan an kwatanta da sauran ofisoshin 'yan sanda a North Wales.

Babban kwanstabul ɗin 'yan sanda, Mark Polins ya ce "kuɗin da za a tara sakamakon rufe ofishin 'yan sandan, za a sake zuba su wajen inganta rayuwar jami'an 'yan sandan yankin."