Soyayya da fursuna ta ja wa ganduroba ɗauri

Prison

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Alkali ya ce Sian Dahorty ta aikata cin amanar aiki.

An yanke wa wata jami'ar gidan yari wadda ta sumbata kuma ta yi musayar wasiƙa da wani fursuna mai kisan kai, hukuncin zaman gidan yari saboda aikata ba daidai ba a ma'aikatar gwamnati.

Sian Doherty, mai shekara 24 ta gamu da Michael Dobson ta hanyar aikinta a gidan yarin HMP Gartree cikin watan Satumban 2015 a Burtaniya.

Wata kotun Leicester ta saurari yadda Michael Dobson ya aika wa gandurobar saƙwanni har da "kalaman batsa", a lokacin da kuma ita ta riƙa kiran shi "rabin raina" a zantawarsu ta wayar tarho.

An dai ɗaure Sian Doherty wata shida a gidan yari bayan an same ta da laifi.

Asirin gandurobar ya tonu ne lokacin da aka riƙa nuna damuwa kan yadda Michael Dobson yake soyayya da wata ma'aikaciya.

Dobson, wanda ke zaman ɗaurin aƙalla shekara 16 saboda laifin kisan kai, ya riƙa aika saƙwanni ga Sian Doherty - wadda ke amfani da sunan Holly Smith - ciki har da wani da ke cewa: "Kina sanya ni nutsuwa yarinya."

A wani saƙon, Michael Dobson ya ce mata: "Na ƙagu ki kawo mini ziyara don mu sumbaci juna tsawon sa'a biyu".

Da yake yanke hukunci, Mai shari'ah Nicholas Dean ya faɗa wa gandurobar: "Ga alama, kamar yadda na fahimta, kin riƙa nuna tirjiya, a wani ɓangare saboda hatsarin da za ki shiga idan aka gano, a wani ɓangaren kuma ke da kanki kin san ana shirya miki gadar zare ce.

"Wannan aikin gwamnati ne mafi muhimmanci da gaske. Amanar da aka ba ki tana da ɗumbin muhimmanci."