Za a bai wa masu shirin haihuwa ƙarin kuɗi a India

Pregnant woman Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu na ganin yawan bai wa matan hutu zai janyo musu matsala a wurin aiki.

Majalisar dokokin kasar India ta zartar da wata doka da ta bai wa mata ma'aikata masu juna biyu hutun mako 26 daga wanda suke yi na mako 12 a yanzu tare da biyansu albashi.

Dole ne dukkan kamfanin da ke da ma'aikata fiye da goma ya yi aiki da sabuwar dokar.

Ministan kwadago na kasar Bandaru Dattatreya ya ce an kirkiro dokar ne domin zama wata kyauta da yin "godiya ga mata".

India ta zama kasa ta uku a duniya da ta fi bai wa mata hutun haihuwa mafi tsawo, bayan Canada da Norway, wadanda ke bai wa matan mako 50 da mako 44 kowaccen su.

Wannan kudurin doka shi ne na farko da majalisar dattawa ta amince da shi a shekarar da ta gabata, wanda a yanzu ya zama doka bayan majalisar wakilai ta amince da shi.

Masu fafutika sun ce dokar za ta karfafa wa mata gwiwa su rika yin aiki ko da suna da juna biyu.

Wani bincike da wata kungiya ta gudanar a shekarar da ta wuce ya gano cewa daya bisa uku na matan kasar suna barin aiki da zarar sun haihu.

Labarai masu alaka