Alkali ya ki haramta wa Trump hana baki shiga Amurka

An ci gaba da zanga-zanga domin kyamar matakin Trump Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An ci gaba da zanga-zanga domin kyamar matakin Trump

Wani alkalin Amurka ya ki bayar da umarnin hana aiwatar da sabon shirin shugaban kasar Donald Trump na hana baki shiga kasar.

Wannan alkaki na kotun gunduma ta Seattle James Robart, shi ne alkalin da a baya ya yanke hukuncin hana shugaban kasar aiwatar da matakinsa na kin barin 'yan wasu kasashen Msulmi shiga kasar.

Alkali Robart ya gaya wa lauyoyi su kawo kwararan hujjoji idan suna so ya amince da bukatunsu.

A ranar Alhamis ne dai shirin Trump na dakatar da 'yan kasashe shida shiga kasar tsawon kwana 90 nan take ya soma aiki, amma ya samu tsaiko saboda matakin da wasu jihohi suka dauka na kalubalantarsa a gaban kotu.

Lauyoyi a jihar Washington sun bukaci alkali Robart ya tsawaita haramcin da ya yi wa Trump na hana 'yan kasashen Musulmin shiga kasar.

Sai dai alkalin ya ce ba zai iya yin haka ba, yana mai kafa hujja da wasu tsare-tsare.

Ya kara da cewa dole ne a gabatar da wasiu karin hujjoji idan ana so ya gamsu da bayana lauyoyin.

Labarai masu alaka