Harin bama-bamai ya kashe 'yan Iraqi 40 a Syria

Wurin ya yi kaca-kaca da jini Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wurin ya yi kaca-kaca da jini

Wani harin bama-bamai da aka kai a Damascus, babban birnin kasar Syria ya yi ajalin 'yan Iraqi 40 kana ya jikkata 120, a cewar gwamnatin ta Iraqi.

An kai harin ne kusa da makabartar Bab al-Saghir, wacce ake binne mabiya Shia, kuma an ce an hari mutanen da suka je makabartar domin yi wa waliyyai addu'a ne.

Mabiya Sunna kan kai wa 'yan Shia hare-hare amma ba su cika kai musu hari a babban birnin kasar ba.

Wata yarjejeniya da Rasha ta taimaka wajen kullawa tare da hadin bakin Turkiyya da Iran ta soma aiki tun ranar 30 ga watan Dismaba, amma dai ba a daina kai hare-hare ba.

An yi tattaunawar zaman lafiya sau biyu, inda kuma ake sa ran yin wata tattaunawar a makon gobe.

Akasarin yankunan Damascus na karkashin gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad, sai dai 'yan tawaye na rike da wasu sassan birnin.

Har yanzu ba a san wadanda suka kai wannan hari ba, wanda kakakin ma'aikatar wajen Iraqi Ahmed Jamal ya bayyana a matsayin wani "laifi da 'yan ta'adda suka aikata".

Hotunan da aka dauka sun nuna yadda wurin ya jike da jini.

Labarai masu alaka