Kiwo ya rinjayi karatu a Nijar

Jamhuriyar Nijar

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Bushewar ciyawa ya sa dumbin makiyaya na yin kaura da iyalansu abin kuma da ke shafar ilmin dubban yara.

Hukumar ba da agaji ta duniya ta ce rashin abincin dabbobi a wasu sassa na jamhuriyar Nijar ya sanya rufe kusan kashi 50 cikin 100 na makarantun boko, inda sama da dalibi dubu 33, galibi 'ya'yan makiyaya suka aske karatu.

Hakan na faruwa ne sakamakon wani fari da ake fuskanta wanda kuma ya haddasa rashin ciyawar dabbobi, don haka makiyaya ke kwashe 'ya'yansu zuwa wasu sassa masu yalwar ciyayi.

Ta ce dumbin makiyaya ne bushewar yanayi ya tilasta wa yin kaura da dabbobib da iyalansu.

A yankin Katsinar Maradi da ta Damagaram, da ke bangaren tsakiya-maso-gabashin Nijar da kuma Agadez da ke arewacin kasar da na Tawa a Yammaci, kididdiga ta nuna cewa an rufe makarantun boko da dama.

Shugaban kungiyar makiyaya ta Burtal Brode da ke gundumar Bermo a jihar Dakwaro yankin Katsinar Maradi ya shaida wa BBC cewa a wajensu ne lamarin ya yi muni.

Ya ce '' Iska ce ta yi yawa, tsawon kwana bakwai tana kadawa da karfi, mun sanar da hukumomi sun ce gwamnati za ta yi kokarin taimaka wa makiyaya''.

A cikin watan Janairun 2017 ne gwamnatin Nijar ta sanar da cewa kasar na fama da karancin abincin dabbobi kimanin tan miliyan 12 da ake bukata.