Jam'iyyar PDP ta yi wa APC mai mulki baki

Jam'iyyar PDP Hakkin mallakar hoto APC
Image caption Tsagin Ahmed Muhammad Makarfi yana jayayya da tsagin Ali Modu Sheriff a kan shugabancin PDP

Babbar jam'iyyar adawa a Nijeriya PDP ta ce babu mamaki nan da shekara mai zuwa annobar da ta same ta, ka iya auka wa jam'iyyar APC mai mulki.

Shugaban wani tsagi na jam'iyyar ta ƙasa, Alhaji Ahmed Muhammad Maƙarfi ya ce a jira daga farkon shekarar 2018 a ga irin juye-juyen siyasar da za su auka wa APC.

Ya ce su ma wannan al'amari ya faru gare su, inda wani lokaci a baya jam'iyyar PDP ke da sama da jiha 30 a tarayyar Nijeriya, amma da aka yi juyi sai ga shi ta rasa shugabancin ƙasar.

A cewar Maƙarfi "maganar cin zaɓe, ba batu ne kawai na 'yan jam'iyya ba, sai ka yi tunanin abin da masu kaɗa ƙuri'a za su so, za su yi na'am da shi. Idan ka fito da abin da masu jefa ƙuri'a ba za su na'am da shi komai tsarin da ka yi, ba yadda mutum zai yi."

Ya ce adawa ba cinikin jam'iyya ce kawai ba, su ma 'yan ƙasa suna yi. "Saboda kukan jama'a ma shi ne gaskiya, mu idan muka yi magana ma a kan wasu abubuwa sai a ce siyasa muke yi".

Tsohon gwamnan jihar Kadunan, ya ce gaskiya ne rikice-rikice na cikin gida sun sanya jam'iyyar ba ta yin abubuwa yadda ya kamata a ce tana yi, amma dai duk da haka tana yin daidai gwargwado.

Maƙarfi ya ce tsaginsa na amfani da damar da tsarin mulkin Nijeriya ya ba shi ta ɗaukaka ƙara a kan hukuncin kotu (da ya tabbatar da Sanata Ali Modu Sheriff a matsayin shugaban PDP) wanda ba su yarda shi ba.

A cewarsa duk da haka suna bin matakin sasantawa matuƙar za a yi aiki da duka shawarwarin da wani taron gwamnonin jam'iyyar ya cim ma, ba tare da rage komai ba.

Labarai masu alaka