An gudanar da taron 'Matan Saudiyya za su iya'

Wata mace 'yar Saudiyya Hakkin mallakar hoto FAYEZ NURELDINE/AF
Image caption Mata a Saudiyya ba su da ikon tuka mota, kuma suna bukatar rakiyar muharrami

An gudanar da wani gangami a ƙasar Saudiyya da nufin zaburas da 'yan matan masarautar su tashi tsaye don cim ma burukan rayuwa.

Masu jawabi a taron wanda ba a saba ganin irinsa ba cikin birnin Riyadh akwai Raha Moharrak, mace ta farko 'yar ƙasar Saudiyya da ta taka har saman tsaunin Everest mafi tsawo a duniya.

Ta ce jazaman ne 'yan matan ƙasar su san cewa su ba ƙasƙantattu ba ne a kan maza.

Ɗaya daga cikin masu shirya wannan taro mai taken "Matan Saudiyya za su iya" ta ce manufarsu ita ce samar wa 'yan mata maduban koyi.

A ƙarƙashin dokoki da al'adun Saudiyya dai duka mata na rayuwa a ƙarƙashin muharrami kuma ba sa tuƙa abin hawa.