An baza 'yan sanda 100 don neman jaririya a Afirka ta Kudu

South African Baby
Bayanan hoto,

Tun ranar Juma'a ake neman jaririyar 'yan wata ɗya da haihuwa.

'Yan sandan Afirka ta kudu na ci gaba da gudanar da bincike don gano wata jaririya da ta ɓata bayan sace motar iyayenta a birnin Durban ranar Juma'a.

Jaririyar 'yar wata ɗaya, Siwaphiwe Mbambo tana kujerar baya ne lokacin da wasu 'yan bindiga suka shiga kuma suka yi awon gaba da ita a wajen wasu kantuna.

Uwar ta yi ƙoƙarin warto ɗanta mai shekara takwas, lokacin da aka figi motar da Siwaphiwe a ciki.

Daga bisani, 'yan sanda sun gano motar babu kowa a ciki.

Yanzu dai an baza 'yan sanda fiye da 100 don neman wannan jaririya da ɓatanta ya janyo gagarumin gangamin kafofin yaɗa labarai a Afirka ta kudu.