Mai ciki ta yi yunƙurin harin ƙunar-baƙin-wake a Maiduguri

Rikicin Boko Haram ya tagayyara miliyoyin mutane
Bayanan hoto,

Rikicin Boko Haram ya tagayyara miliyoyin mutane

Jami'an tsaro a Maidugiri da ke jihar Bornon Najeriya sun kashe wasu mata da suka yi yunkurin kai harin kunan-bakin-wake a birnin.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Victor Isuku ya fitar na cewa, "mata biyu, masu kimanin shekara 18 ne suka yi yunkurin kunan-bakin-wake, amma 'yan kato-da-gora sun gan su sannan jami'an tsaro sun harbe su har lahira".

Ya kara da cewa matan sun so kutsa kai ne wani wuri ranar Asabar amma Allah bai ba su sa'a ba.

Rahotanni sun ce daya daga cikin matan na da juna biyu.

Ishaku ya ce babu baya ga matan babu wanda mutu ko jikkata, kodayake ma'aikatan agaji sun ce daya daga cikin 'yan kato-da-gorar ya jikkata.

Kungiyar Boko Haram dai na yin amfani da mata sosai wajen kai hare-haren kunar-bakin-wake, inda a kwanakin baya suka fito da salon yin amfani da mata dauke da jarirai domin bad-da-sawu.

Hakan na faruwa bayan rundunar sojin kasar ta ce ta ci karfin su, lamarin da ya sa suka rasa mafada.

Kiyasi ya nuna cewa rikicin kungiyar ta Boko Haram ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 20,000 sanna ya tilasta wa fiye da mutum 2.6m barin gidajensu.