Korarriyar shugabar Korea ta Kudu ta fice daga fadar shugaban kasa

Wani jerin gwanon motyoci ne ya yi wa Park Geun-hye rakiya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani jerin gwanon motyoci ne ya yi mata rakiya

Korarriyar shugabar Korea ta Kudu Park Geun-hye ta fice daga fadar shugaban kasa, kwana biyu bayan wata kotu ta amince da matakin da 'yan majalisar dokoki suka dauka na tsige ta daga mulki.

Ms Park ta isa gidanta da ke kudancin birnin Seoul a yayin da magoya bayan ta ke daga mata hannu.

Ta ce komai daren dadewa gaskiya za ta fito.

An cire ta daga mulki ne saboda hannu a cikin wata badakalar cin hanci da rashawa da ta hada da babbar aminiyarta, Choi Soon-sil.

Masu hamayya da Ms Park, wadanda ke kira a kama ta, da kuma magoya bayan ta sun yi gangami daban-daban a Seoul ranar Asabar.

Yanzu dai Ms Park ta rasa kariyar da kundin tsarin mulkin kasar ya ba ta na hana ta fuskantar shari'a kan zargin da ake yi mata na barin kawarta Ms Choi ta rika amfani da takardun gwamnati wajen kwatar kudi da kuma neman alfarma daga wurin kamfanoni da 'yan siyasa.Ms Park ta fice daga fadar shugaban kasa da misalin karfe 11:00 na safe a agogon Najeriya da Nijar bayan ta yi sallama da ma'aikatan fadar.

Wani jerin gwanon motoci ne ya raka ta gidanta da ke gundumar Samseong.

Daruruwan magoya bayan ta sun taru, inda suka rika daga tutar kasar.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ms Park ta koma gidanta da ke gundumar Samseong
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption An ga ma'aikata na shigar da kayana Ms Park cikin gidanta
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ms Park ta rasa kariyar da kundin tsarin mulki ya ba ta

Labarai masu alaka