Intanit ya zama dandalin karya -Makirkirin intanit

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sir Berners-Lee ya ce zai yi kokarin ganin an yi wa mutane adalci wajen ba su iko na tsare bayanan sirrinsu a intanit

Mutumin da ya kirkiri hanyar intanit ta www, Tim Berners-Lee, ya nuna damuwa game da yada labaran karya da kage a shafukan intanit, da rashin tsare bayanan sirri na masu shiga intanit, da kuma amfani da damar yada manufofin siyasa ta hanyar da bata dace ba a shafukan na intanit.

Cikin wani sako domin alamta cika shekaru 28 da kirkiro hanyar intanit din ta www wato World Wide Web, ya yi gargadi game da yadda mutane ba su da iko a kan bayanansu na sirri a intanit da kuma yadda gwamnatoci ke sa ido da bin diddigin talakawansu a shafukan intanit tare da sanya masu takunkumi a wasu lokutan.

Ya ce shafukan da aka kirkiro domin biyan bukatun jama'a, sun koma yada bayanan karya da labaran kage tamkar wutar daji.

Tim Berners-Lee ya kuma yi kiran a kalubalanci wuce gona da iri na gwamnatoci wajen kafa dokokin sa ido kan shafukan intanit, kana a yi kokarin magance matsalar yada bayanan da ba daidai ba, ko na karya, ko kuma na dulmiyar da al'uma da gangan.

Makirkirin intanit din ya ce yana da wani shiri na shekaru biyar da nufin dakile wadannan matsaloli. Sir Berners-Lee ya kara da cewa za a karfafa gwiwar shafukan sada zumunta na zamani su dakile yaduwar bayanan karya.

Ya kuma kara da cewa kamfanonin sadarwar a intanit ba su bai wa masu amfani da intanit din damar da ta kamata wajen bayyana masu irin bayanan sirri na kashin kansu da basa so a yada, kuma ka'idodjin tsare sirrin masu shiga intanit tamkar na je-ka-na-yi-ka ne.