Shinkafa ta fi fetur a arzikin Nigeria — Gwamna Atiku

Nigeria Rice
Image caption Shinkafa ta kasance abinci a gama-gari

Yanzu ga alama babu abinda ya fi damun talaka a Najeriya, kamar batun kayan abinci da tsadarsa, ko da ya ke dai gwamnatoci da daidaikun mutane da dama a kasar na cewa an dade ba a yi noma musamman na shinkafa mai yawa irin na bana ba.

To sai dai gwamnan jihar Kebbi dake arewacin arewacin kasar, Alhaji Atiku Abubakar Bagudu, ya ce bisa hasashensu arzikin dake cikin noman shinkafa a Nijeriya ya fi wanda kasar ke samu daga man fetur. A halin yanzu tattalin arzikin kasar ya dogara kusan kacaukam a kan man fetur ne.

Alhaji Bagudu ya ce sau uku ake noman shinkafa cikin ko wace shekara, kuma idan aka dage, to kasar zata rika sayar wa kasashen Afirka da sauran duniya shinkafar.

Ya yi ikirarin cewa a bana an noma kimanin ton 3,000 000 na shinkafa a jihar ta Kebbi sakamakon hadin gwiwa na masu ruwa da tsaki a ciki da wajen jihar, kuma ana fatan nan gaba adadin zai fi haka.

Gwmnatin Nijeriya dai ta ce ta himmatu wajen tabbatar da wadata kasar da abinci yayin da gwamnatocin jihohi su ma ke cewa suna nasu kokarin.

A baya-bayan nan gwamnatocin jihohin Kebbi da Legas sun yi noman shinkafa na hadin gwiwa a cikin jihar Kebbi, suka kuma fara yunkurin sayarwa a kasashen waje.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jihohin Kebbi da Legas sun yi hadin gwiwa kan bunkasa noman shinkafa

Gwamna Bagudu ya shaida wa wakilin BBC Umar Shehu Elleman a Legas cewa fitar da shinkafa zuwa kasashen waje daga Nijeriya zai bai wa kasar damar samun kudaden shiga fiye da kudaden da ta ke samu yanzu daga albarkatun man fetur.

''Da ya ke wurare da dama a Nijeriya, sau uku ake noma shinkafa ga shekara, mu burinmu (shi ne) ya kasance kasashen Turawa, da kasashen Asiya ma, da kasashen Larabawa, daga gare mu su ke saye'', inji gwamna Bagudu.

Gwamnan ya kuma yi watsi da fargabar da wasu ke nunawa cewa sun fara fitar da hsinkafar zuwa kasashen waje alhali gida bai wadata ba, yana mai cewa kasar na da dukkan albarkatun noma da zata iya amfani da su domin rike kanta, kuma gwamnati za ta ci gaba da nuna kwazo a nata bangaren. Ya kuma bukaci 'yan Nijeriya da su kara rungumar noma.

Shinkafa na daya daga cikin nau'o'in abinci da 'yan Nijeriya suka fi ci inda a duk shekara al'umar kasar ke cin muliyoyin ton na shinkafar, wadda galibi daga kasashen waje ake shigo da ita.

Image caption An dukufa noman shinkafa a kudanci da arewacin Nijeriya

Masharhanta da dama dai na ganin akwai jan aiki a gaban Nijeriya na wadata kanta da abinci, kafin ma a yi batun fitarwa zuwa kasashen waje.

Galibin manoman kasar ba su da kayan aiki na zamani, kuma tsare-tsare da manufofin gwamnati ba kasafai su ke dorewa ba.

Ministan noma na Nijeriya, Mista Audu Ogbeh, a kwanakin baya, ya shaida wa BBC cewa kasar kan kashe kimanin dala muliyan biyar a ko wace rana, wajen shigowa da shinkafa daga kasashen waje. Wasu alkaluman kuma sun nuna cewa takan kashe kimanin naira biliyan 500 a duk shekara wajen shigowa da shinkafar daga kasashen waje musamman na nahiyar Asiya da kudancin Amurka.