Nigeria za ta yi zaman a yi ta ta ƙare da Afirka ta Kudu

Majalisar Dokokin Najeriya
Image caption 'Yan majalisar dokokin Najeriya za su gana da takwarorinsu na Afirka ta Kudu kan kyamar baki

Wani ayarin majalisar wakilan Najeriya na musamman yana kan hanyar zuwa Afirka ta Kudu ranar Litinin don bin kadin `yan kasar waɗanda hare-haren nuna ƙyamar baƙi suka ritsa da su a baya-bayan nan.

Ayarin dai na fatan tattaunawa da takwarorinsu 'yan majalisar Afirka ta Kudu domin lalubo hanyar magance wannan matsala.

A makwannin baya ne aka far wa `yan Najeriya a Afirka ta kudu, inda aka kona musu dukiya mai yawa.

Hon. Shehu Aliyu Musa na cikin ayarin, kuma ya shaida wa BBC cewa za su gana da hukumomi gami da takwarorinsu na Afirka ta Kudu, da 'yan Najeriya da ke zaune a can domin jin irin kalubalen da suke fama da shi.

Sai dai Hon Shehu Aliyu Musa ya kara da cewa duka abin da ke faruwa a ko wacce kasa ana la'akari da dokoki ne, wadanda su suke sa wa a yi ko kuma hanawa a yi .

Don haka ya ce za su shawarci Afirka ta kudu kan dokokin da ya kamata ta ɓullo da su a kasarsu idan ba su da masaniya, domin hana sake aukuwar wannan al'amari da bai dace ba, a cewarsa.

'' Wannan lokaci ne za mu fada musu cewa ya isa, ya isa irin abubuwan da ke faruwa a kan al'ummarmu a Afirka ta Kudu, saboda ba ma son lalacewar dangantaka''.

Wannan dai ba shi ne karon farko da irin wannan al'amari na kyamar baki ke faruwa a Afirka ta Kudu ba.

Labarai masu alaka