Paris: Za a kashe maƙudan kuɗi don sayo tarkunan ɓera

Beraye sun addabi Paris
Bayanan hoto,

Akwai akalla bera biyu a kowanne gida da ke birnin Paris

Magajiyar birnin Paris, Anne Hidalgo ta bayar da sanarwar ɓullo da sabbin shirye-shiryen taƙaita ƙaruwar ɓeraye da kuma raba titunan birnin da guntattakin taba sigari.

Yayin zantawa da wata mujalla mai fita mako-mako, Ms Hidalgo ta ce birnin Paris zai kashe dala miliyan ɗaya da dubu 600 don sayo sabbin tarkunan ɓera da kuma kafa ture-ture na jefar da guntun taba sigari.

Ƙiyasi ya nuna cewa akwai akwai ɓera ƙwaya biyu a kowanne gida da ke birnin Paris.

Mahukuntan Paris dai sun rufe wasu dandali da lambuna cikin watan Disambar bara a wani ɓangare na yaƙi da ɓeraye.

Magajiyar birnin ta kuma buƙaci gidajen abinci da gine-gine su sanya ƙarin ture-ture a ƙofofin shigi da ficensu don yar da sauran taba.

Duk shekara ma'aikatan birnin Paris na kwashe sama da tan 150 na guntun taba sigari.