Nigeria: Buhari zai karɓi ragamar aiki

Hakkin mallakar hoto NIGERIAN GOVERNMENT
Image caption Muhammadu Buhari zai bi sannu a hankali wajen ci gaba da harkokin mulki bayan komawarsa Najeriya daga jinya

Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari zai koma bakin aiki ranar Litinin ɗin nan, bayan ya shafe kwana hamsin yana jinya a London.

Da safiyar ranar Juma'ar da ta gabata ne, shugaban ƙasar ya koma gida, sai dai ya ce mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo zai ci gaba da tafiyar da al'amura a ranakun ƙarshen mako.

Mai magana da yawun shugaban, Garba Shehu ya ce gabanin ya shiga ofis, Muhammadu Buhari zai aika wasika ga majalisar dokokin kasar don shaida mata komowarsa gida da kuma karbar mulki a hukumance.

Ya ce suna fata shugaban zai bi a hankali bayan jinyar da ya yi ta tsawon kwana hamsin.

A cewarsa shugaba Muhammadu Buhari zai ɗan ɗauki lokaci wata ƙila kafin ya iya ci gaba da aiki wurjanjan kamar da ya saba yi a baya ba.

Wasu 'yan Nijeriya dai sun yi ta bayyana cewa harkokin mulki sun fi kyautatuwa lokacin da mataimakin shugaban, Farfesa Yemi Osinbajo yake riƙo.

Shi dai Osinbajo ya riƙa kai ziyara zuwa sassan ƙasar da kuma ɓullo da wasu matakai waɗanda ake ganin sun taimaka wajen farfaɗo da darajar Naira.

A tsawon lokacin riƙon, Nijeriya ta ga raguwar fasa bututan man fetur a yankin Naija Delta mai arziƙin man fetur.

Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto NIGERIAN GOVERNMENT
Image caption Muhammadu Buhari zai bi sannu a hankali wajen ci gaba da harkokin mulki bayan komawarsa Najeriya daga jinya

Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari zai koma bakin aiki ranar Litinin ɗin nan, bayan ya shafe kwana hamsin yana jinya a London.

Da safiyar ranar Juma'ar da ta gabata ne, shugaban ƙasar ya koma gida, sai dai ya ce mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo zai ci gaba da tafiyar da al'amura a ranakun ƙarshen mako.

Mai magana da yawun shugaban, Garba Shehu ya ce gabanin ya shiga ofis, Muhammadu Buhari zai aika wasika ga majalisar dokokin kasar don shaida mata komowarsa gida da kuma karbar mulki a hukumance.

Ya ce suna fata shugaban zai bi a hankali bayan jinyar da ya yi ta tsawon kwana hamsin.

A cewarsa shugaba Muhammadu Buhari zai ɗan ɗauki lokaci wata ƙila kafin ya iya ci gaba da aiki wurjanjan kamar yadda ya saba yi a baya ba.

Wasu 'yan Najeriya dai sun yi ta bayyana cewa harkokin mulki sun fi kyautatuwa lokacin da mataimakin shugaban, Farfesa Yemi Osinbajo yake riƙo.

Shi dai Osinbajo ya riƙa kai ziyara zuwa sassan ƙasar da kuma ɓullo da wasu matakai waɗanda ake ganin sun taimaka wajen farfaɗo da darajar Naira.

A tsawon lokacin riƙon, Najeriya ta ga raguwar fasa bututan man fetur a yankin Naija Delta mai arziƙin man fetur.

Labarai masu alaka