'Buhari ya mutunta kundin tsarin mulki'

'Yar aduwa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A lokacin da shugaba 'Yar aduwa ke mulki ya tafi jinya ba tare da ya mika ragamar ga mataimakinsa ba

Tun bayan tafiya da dawowar shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zuwa London yin hutun jinya, aka yi ta samun ce-ce-ku-ce a kasar, duk kuw da cewa kafin ya tafi sai da ya mika ragamar shugabanci ga mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.

Wasu masu sharhi kan al'amuran yau da kullum dai na ganin shugaban ya yi matukar kokari kuma ya girmama kundin tsarin mulki wajen mika ragamar mulkin ga Farfesa Yemi Osinbajo.

Dr Jibrin Ibrahim mai sharhi ne kan al'amuran yau da kullum, a wata hira da ya yi da BBC ya ce, "Abu na farko shi ne shugaba Buhari ya bai wa kundin tsarin mulki daraja kwarai da gaske, tunda da tafiyar ta taso ya yi abin da ya kamata."

"Ya bayar da mulki, bai yi yadda wasu suka yi a baya ba, wadanda basa yarda su bayar da ragamar mulkin. Kuma yanzu ya je ya samu magani ya ji sauki ya dawo, To abin da ya kamata a yi kenan, kuma hakan ya yi," in ji shi.

Dakta Jibrin ya kara da cewa, "Da ya dawo din ma, bai nuna cewa mulkin ne ya dame shi ba. Har ya yi bayani cewa mataimakin nasa ya ci gaba da mulki har sai ranar Litinin, wanda zai mika wasika gurin majalisa ya ce, ya dawo yanzu, ya shirya, zai ci gaba da mulki."

A don haka Dakta Jibrin ya bayyana shugaba Buhari a matsayin mutum wanda ya san ya kamata, kuma ya aikata abin da ya kamata.

Da yake magana kan batun ko me ya sa shugaban yake boye irin yanayin rashin lafiyar tasa, sai ya ce, "Ya kamata mu tuna rashin lafiyar mutum ba abu ba ne da lallai sai ya fallasa duniya gaba daya ta sani.

Abin da kundin tsarin mulki ya fada shi ne, in dai rashin lafiya ta kai inda ba za ka iya aikinka na mulki ba, shi ne dole ka fada, ga abin da ka ke ciki, don wani ya hau kai, to tun da rashin lafiyar tasa ba ta kai wannan ba, ba lallai ba ne sai ya fada wa duniya abin da ke damunsa."

'Muhimmancin dawowarsa'

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Buhari ya ce nan da makonni kadan zai koma ganin likita a London

Dakta Jibrin ya ce dawowar shugaban na da muhimmanci sosai bayan cece-kucen da aka yi ta samu, "Tun da an yi ta maganganu iri-iri wasu ma sun ce ya rasu, da sauransu, dawowar tasa ta karyata su kenan, kuma ya nuna wa duniya gaskiya rashin lafiya ya yi, kuma ya samu sauki."

Ya kuma ce dawowar tasa za ta ba marada kunya wadanda suke son jawo bambanci tsakanin sa da mataimakinsa, "Ita kuma wannan magana ba ta da hujja tun da kowa ya sani tun da suka fara mulki, aikin nan tare suke yi, ba wai wani ya fi wani ba."

"Shi shugaba Buhari, mutum ne wanda tun ma zamanin da ya yi mulkin soja, ya nuna wa duniya cewa wadanda suke aiki da shi, tare za su yi mulkin nan," in ji Dakta Jibrin.

Wannan dai shi ne karo na uku da shugaba Buhari ya mika ragamar mulkin kasar ga Farfesa Osinbajo, tun bayan da suka sha rantsuwar mulki a watan Mayun 2015.

Karo na farko shi ne a watan Fabrairun 2016 lokacin da shugaba Buhari ya tafi hutun kwana biyar, sai kuma a watan Yunin 2016 da ya je ganin likita sa Birtaniya, sai kuma na baya-bayan nan a watan Janairun 2017 da ya sake daukar hutu inda daga bisani ya tsawaita hutun don kammala wasu gwaje-gwajen lafiyarsa.

Labarai masu alaka